Saturday, 14 July 2018
Jarumi Abbas Sadik Wanda Ya Hada Baiwa Ukku A Harka Fina finan kannywood

Home Jarumi Abbas Sadik Wanda Ya Hada Baiwa Ukku A Harka Fina finan kannywood
Ku Tura A Social Media
ABBAS SADDIK, ya kasance Jarumin finafinan Hausa da na Turanci. Masana tarihin farfajiyar harkokin masana’antar fim, sun bayyana shi a matsayin wanda har kwanan gobe babu wani jarumi a bangaren fim din Hausa ko Turanci, da yake fim da manyan harsuna uku na duniya. Shi kadai ne a cikin sahunsu Allah ya hore ma fasahar fitowa a cikin finafinai na Hausa, na Turanci da kuma fim din Larabci. Sannan ya kasance wanda ya fi kowane jarumin finafinan Hausa da Turanci dadewa tauraronsa bai dakushe ba, domin har kwanan gobe ana kan damawa da shi, sannan an bayyana shi a matsayin jarumin da yake da haddar Alkur’ani mai girma tun yana dan shekara 16, sannan ya taba lashe gasar karatun Alkur’ani tun yana dan shekara 14.
Wakilinmu, IBRAHIM IBRAHIM, ya sami damar zantawa da shaharararen jarumin kamar haka:

Zai yi wa masu karatu dadi ka fara bayyana musu ko wane ne Abbas Saddik saboda waka a bakin mai ita ta fi dai?

Suna na Abbas Saddik, ni haifafen Jihar Kaduna ne, an haifeni a shekarar 1979, na yi karatun Firamari na a st wrizer primary school, sannna na wuce makarantar Sakandire dina a laranto, daga nan na wuce Jami’ar Jos, a inda na karanta sashin lissafi, wato accounting. Bayan na kammala karatu na sai na tsunduma sana’ar fim.

Ya aka yi ka tsinci kanka a harkar flm?

Natsinci kai na ne a harkan fim tun ina shekara shida lokacin Mahaifina ya na aiki a NTA Jos, inda za a yi wani shiri na Yara, wanda Yara za su fito a cikin dirama na Hausa ko na Turanci, ya na zuwa ya kaini a sani a ciki, a kwai wani shiri da ake yawan gani na a ciki, misali akwai irin na Yara a lokacin Kirsimati ko Sallah, akan bani wani dama nayi wani abu a ciki, wanda zai zamanto abin koyi ga Yara idan suna kallo, sannan malamaina na makarantu sun fahinci ina da baiwa a kan wasan kwaikwayo da waka, tun lokacin ina makarantar firamari, da sakandare har da ma Islamiyyanmu. Lokacin muna Islamiyya akwai diramar da muke shiryawa ana dauko kissan Sahabban Manzan Allah (SAW), muna yin shi a dirama da kissan abubuwan da suka faru a lokacin Annabwa, sai dai ba za ace ga Annabin ba, amma za a bayyana wasu su nayi na wasu Sahabbai na Annabi Muhammad (SAW), annabinne kawai ba’a nuna wa, amma za ace Annabi yace ayi kaza da kaza.

Ko shigar ka Jami’a ta kara maka kaimin harkar fim?

Eh, ai ko a lokacin ina makaranta idan a na naima na, ko a same ni a wurin ‘yan mass comm, ko ‘yan theater art, duk sune Abokaina, saboda muna hadaka wajen wasu abubuwa da suka shafi wasan kwaikwayo, kamar dirama, wasan kwaikwayo na makarantu, drama wanda ake gayyato fitattun mawaka na kudu, ba zan manta ba, akwai lokacin da na tsinci kai na a saman ‘stage’ tare da su Idrees Abdulkareem, 2 face, tun lokacin suna Plantation Boys, su P-Skure, tun basu fara waka ba, suna kwaikwayon wakokin Micheal Jacson, tun a wannan lokaci ina da baiwan waka da dirama.

Katamaime yaushe ne ka fara fim baya ga wasannin dirama?

Na fara shi ne lokacin da aka fara home bidiyo a Nijeriya, a Jos a aka fara daukar shirin zuwa lokacin an yi fina-finai da damar gaske a Jos, kaman irin su Return to Kazondia, Iber Silber, Eleben Hour, da Show Dawn, da kuma fim din laraba, duk na fito a cikinsu, kenan tun kamin a fara yin fim din Hausa , a kwai fim din Amina wanda na sami matsayi mai kyau, na fito a fadar Sarki a cikin shirin fim din. Saboda haka ni na fara yin shirin fim din Turanci kafin na Hausa.

Da wane fim ka fara?

Lokacin da aka fara shirin fim din Hausa, sai na ga ina da ra’ayi fim din Hausar, sai muka fara yin sa s jos, Alhaji Yusuf Khalid shirya wani fim mai suna Rigar Kaya, fim din Nazari, wanda shahararrun ‘yan fim a wancan lokacin irin su Sulaiman Sa’id, duk sun fito a ciki, amma shirin da na fara fitowa a ciki na farko wanda kuma ni na ja ragamar shirin fim din shi ne, a Kera, wanda a yanzu zai kai kimanin shekara 18, amma bana san ya shekarun da nayi a jos, a cikin shekarun fara fim dina ina fara kirgawane a lokacin da na koma Kano a 2000, naje kamfanin FKD a mastayin kostum, wato mai bayar da kayan sawa, har na zama mataimakin mai bayar da umurni, a nan na sami cikakken horo, na kara bude ido sosai a harka fim, har na shirya fim dina na farko wanda ni na shirya kuma na bayar da umurni nayi komai, fim din da a ke kira da suna ‘Ikama’. Bayan shi ne nayi fim din Albashi, wanda daga wannan lokacin ne Allah ya haskaka taurarona har duniya ta sanni sosai.
Wadanne kalubale ne ka fuskanta?
Kalubalen da na fuskanta daga farko shi ne, a nayin abinne saboda sha’awa mutum bai isa yace abiyashi ba, sai masu shirya fim suce role kaza ga abin da za a biya in dai akayi kastin din ka a ciki, amma kai ba ka so ayi maganar kudi in dai kai kasamu daman ka fito a ciki bukatarka ta biya, domin kai ba maganar kudi kake yi ba. Lokacin ina FKD ni kostum ne, idan Ali Nuhu ya sami aiki zai ce to kaza za abiyani a mastayinsa na darakta wato mai bayar da umirni, dana zama mataimakin mai bayar da umurni, a lokacin an san abin da ake biyana. Na kai shekaru hudu a kamfanin FKD, kamin Allah yasa na samu jari, kuma na samu daman da zan iya yin fim din kai na. Amma Cikin kalubalen da na fuskanta daga farko akwai maganar kudi, sannan an sha wahala saboda kayan aikin abin da za ka iyayi a cikin minti biyu yanzu, amma a da sai ka dauki tsawon mintuna 30, kamin a yi shi.

Ko za ka yi tsokaci kan nasarorin da ka samu a fagen fim?

Na farko shi ne, ina cin gashin kai na, na samu kai na a inda nakeson ganin kai na, harkan fim harka ne wacce nakeso ina da ra’yi a kansa, saboda haka ni ban sami kai na ina fadi tashin naiman abin da zan yi ba, tun kamin na kammala karatuna na san cewa ga sana’ar da zan yi da izinin Iyayena, kuma suna sona da shi, saboda sun san cewa ina da baiwar da Allah ya hore mun, sun karfafamin gwiwa a kan in yishi. Na biyu kuma na sameshi sana’a ne a saukake tun ina Dan karami na bude ido da yanda akeyin shi, ba abu ba ne dana koya da girmana ba, na uku sana’ce awurina sabo da tun ina Karami a na biyana, misali, na gidan TB komin karancin aikin da akayi za a biyaka, sannan da na girma bana daga cikin wadanda idan an naime su aiki a ce baza a biya su ba.

Wane matsayi ka fi so a saka ka a cikin fim?

Duk matsayin da aka bani na karanta na ga ya dace dani, kuma ba zai zubar min da mutunci na ba, duk matsayin da na karanta na ga yamin dadi inasonsa. Ba ni da wani matsayin da na fison na fito a ciki, domin idan an bani wanda bai min ba, na kan yi magana domin na bukaci a canja min, idan kuma aka ki sai na hakura da aikin gaba daya. Misali na yiwa Iyayena alkawarin ba zan taba fitowa a Dan Daudu ba.

Ko za ka iya kididdige yawan finafinan da ka yi zuwa yanzu?

Wannan lissafi zai mun matukar wuyan kawo wa, dalilina shi ne, tun ina kirgawa har nazo na dai na saboda sun yi yawa, a kwai lokacin da na kirga fim 150 zuwa 300. Domin ko fim din da na fito sau daya ne ina lissafawa da shi, ba zai lissafu ba ne, saboda abu ne da kullum ka keyi kuma kake ciki. Amma akwai kuma wadanda nayi su kuma na fi son su, sun fi kwanciyamin a rai, kamar irin su Albashi, shi ne tun lokacin dana fara nunawa mutane suka sanni har Allah ya dagani, duk inda naje mutane na murna suna so su ganni ido da ido. Ba zan taba mantawa da wani rana ba, naje wani biki, ashe mutane na kaunar gani na fiye da zato, domin a wannan lokacin sai da aka kulleni a cikin wani daki, saboda dimbin mutanen da keson gani na, domin a lokacin ba a dade da sakin fim din Gidan Iko ba, sannan akwai wani shirin fim mai suna ‘Jituwa’ wanda ake nunawa a gidan TB, shi kuma series ne saboda ba wani fim wanda mutane suka kama suna na kamar a wannan fim din ba, wato Dakta Jamal.

Mene ne burinka farfajiyar finafinan Hausa?

Abin da nakeson zama shi ne, na zama mutumin da zai wanye da duniya lafiya, duk abin da mutum yake naima na samu, domin Allah ya hore mun dimbin jama’a, ban yi aure ba na shigo harkar fim, amma yanzu ina da Mata da Yara na uku, ina da Gida da na mallaka, motocin hawa ban san guda nawa na canja ba, duk a sandiyar harkar fim na zama Ambassada na kamfanin MTN, bayan haka kuma ina sana’ar yin MC na bukukuwa dana taro, ina waka kuma wako kina suna ma’ana sosai, mutane suna son su, babu ranar da idan na tashi zan dinga tunanin ina zanje, domin kamin ma ranar tazo ina da abin da zan yi. To ka ga babu abin da da mutun zai so sai dai Allah yasa a gama da duniya lafiya, sana’anrmu ya zama hanya ta naiman Aljanna, ba duniya kawai ba, ni ina yi bawai domin a ganni a TB ne kawai ba, shiyasa ba kowa ne irin fim na keyi ba, idan na ga fim bai dace dani ba, ba nayi saboda duk abin da nake naima na zama a fim, Allah yasa na zama.

Wace shawara kake da ita ga abokan sana’arka ‘yan fim?

Shawara na ga ‘yan uwana ‘yan fim shi ne, duk abin da mutum zai yi ya tuna ba mutum ba ne kawai yake kallonsa, Allah ma yana kallonsa, kar muyi kokarin birge mutu, muyi fim domin Allah ya bamu lada, kar fim ya zamanto mana kawai sana’a, na naiman kudi, mu dauki fim a mastayin abin da idan mun yisa Allah zai bamu lada, kar mu naimi duniya kawai da fim, mu naima har da lahira ma da shi, za mu iya naiman lahira da fim idan har muka fadakar da mutane abin da ya kamata. Mu yi ta dauko zahiri mu saka a ciki wa’azin da za kayi a fim, sai Allah ya sanya ka a Aljanna, muyi kokari a cikin duk fim din da za muyi mu dauko wani a abu daya shafi mutane a addinance, amma ba kai tsaye ba, tun da ba kowa ba ne ya keso ka fito kanuna masa kana yin wa’azi.

Malam Abbas Saddik mun gode.
Godiya ya kara tabbata ga Allah (SWA), sannan godiya ta musamman a gare ku. Na gode da wannan dama da kuka ba ni.

Hirar da jaridar leadershipayau sunkayi da jarumin kenan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: