Wednesday, 25 July 2018
Fitattun Jarumai Mata 7 Da Suka fi tsayda a Duniyar Fim Din Hausa

Home Fitattun Jarumai Mata 7 Da Suka fi tsayda a Duniyar Fim Din Hausa
Ku Tura A Social Media
A satin da ya gabata ne dai muka kawo maku jerin jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da suka kere sana'annin su wajen tsada idan har mutum na son su fito a fim din sa. To a wannan karon ma kuma gamu dauke da jerin jarumai mata a masana'antar da suka fi sauran abokan sana'ar ta su tsada har mutum na son su fito a fim din sa.

 Wannan dai hasashe ne da muka yi bayan wani bincike na musamman da muka gabatar a masana'antar tare kuma da bin kadin wasu sabbin fina-finan da jaruman suka yi a 'yan kwanakin nan. Duk da dai cewa jaruman kan rage kudin da suka caji akan wasu manyan furodusoshin da masu ruwa da tsaki a harkar watakila saboda mu'amalar da ke tsakanin su, wannan jerin sunayen an yi shi ne ba tare da la'akari da hakan ba.

 1. Rahama Sadau

2.Nafisa Abdullahi

 3. Hadiza Aliyu Gabon

 4. Fati Washa


5. Halima Atete

 6. Aisha Aliyu Tsamiya

7. Hafsat Idris barauniya.

Sources:naijhausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: