Thursday, 19 July 2018




Duk Me Bina a Shafin Sada zumunta Saboda Buhari dyaga Yau Ya Dena~Nazir Ahmad Sarkin Waka

Home Duk Me Bina a Shafin Sada zumunta Saboda Buhari dyaga Yau Ya Dena~Nazir Ahmad Sarkin Waka
Ku Tura A Social Media

Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad,Sarkin Waka, yayi suna wajan baiwa mutane hakuri akan lamurran dake faruwa musamman a harkar gwamnati,

Sau da dama idan ya wallafa hoto a dandalin shi na sada zumunta yakan rubuta cewa adai kara hakuri ko kuma a ci gaba da hakuri.

To da alama dai shima hakurin na shi ya kare, domin kuwa a wani sako da ya wallafa yace a gayawa APC cewa, an musu laifi, amma ba zasu bayyana lafin ba yanzu tukuna, 

Irin su matasan Arewa duk da gudummuwar da suka bayar amma anyi watsi dasu ba'a gode musu to zasu nuna cewa su haifaffune.

Bayan wallafa sakon sai ra'ayoyin jama'a ya fara kwarara inda wasu suka alakanta wannan magana da Nazir yayi da cewa, mukamin da aka baiwa Rarara ne yayi masa zafi shi yasa yake wannan magana, 
Wasu kuwa sun dauke ta da zafi inda suka rika mayarwa da Nazir din kalamai, har da zagi dake nuna cewa da Buhari yake kuma bai kamata ya sa kanshi a siyasa ba.

Bayan wadannan ra'ayoyi da mutane suka bayyana, Nazir ya mayar da martani inda yace 
wai su dama haka suke?, 
shi fa bai kira sunan kowa ba yace dashi yake amma gashi sun zo suna zagin shi saboda Buhari.

Nazir ya bayar da misali da Bukhari wanda ya rawaito hadisai daga manzon Allah(S.A.W) inda yace, shi kanshi malamai suna hada hadisin shi da ayar Qur'ani suce be inganta ba ballanta na Buhari dake tare da Osinbajo ace ba za'a mai gayara ba a idan yayi kuskure.

Ga masu cewa Nazirun yana hassada ne saboda mukamin da aka baiwa Rarara, ya basu amsar cewa shi bai ma san da wannan magana ba sai a bakinsu, kuma shi Allah ya tsare shi da yin hassada akan abinda zai kare a Duniya, 
yace, ga manyan mutane da zai yi hassada akansu sai Rarara?, 

Ya kara da cewa ko shekara dari zai yi akan mukamin da aka bashi ba zai samu irin abinda ke gare shi ba.

Nazir ya kara da cewa kai duk me binshi a dandalin shi na sada zumunta saboda Buhari daga yau ya daina, sannan kuma zasu zauna ma suyi shawara akan zamansu a cikin jam'iyyar APC tunda abin haka yake.

Sources:Fb/Nijeriya a yau

Share this


Author: verified_user

0 Comments: