Wednesday, 11 July 2018
Dan wasan Nijeriya Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa Rangers

Home Dan wasan Nijeriya Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa Rangers
Ku Tura A Social MediaTun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin kungiyar.

Gwarzon matashin dan kwallon super eagles, Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa kungiyar Rangers da taka leda.
Kamar yadda jaridu suka bayyana, dan wasan zai koma kungiyar ne bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Roma na tsawon shekara daya.Tun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin dan kwallon kungiyar.

Tsohon gwarzon dan wasan kungiyar Liverpool  yace hazikin matashin yana daya daga cikin dinbim yan wasa da suke birge shi. Ya yaba gwaninta da dan Nijeriyan ke nunawa a filin kwallo.

Dan wasan ya sauka filin jirgin sama ta Edinbugh daidai karfe 10 na safiyar ranar Litinin 9 ga wata domin daukar matakai na karshe kan kwantiragin sa da kungiyar.

A rahoton da jaridar Daily Mail ta fitar, tauraron dan kwallon yana jiran takardar aiki na kasar gabanin sa hannu ga takardar kwantiragi.Sadiq Umar wanda ke taka ma kungiyar As Roma na kasar Italiya wasa zai shiga cikin jerin sabbin yan wasan da sabon kocin Rangers ya kawo.

Kai ga yanzu kungiyar Rangers ta siyo yan wasa bakwai. ga sunayen su kamar haka: Scott Arfield, Allan McGregor, Jamie Murphy, Nikola Katic, Connor Goldson, Ovie Ejaria da Jon Flanagan.

Akwai yiuwar bayan Sadiq Umar shima dan wasan tsakiyar kasar Mali, Lassana Coulibaly, zai dawo kungiyar da taka leda bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Angers na kasar Faransa.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga naijhausa.com.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: