Tuesday, 10 July 2018
Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus

Home Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus
Ku Tura A Social Media
Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus, abin da ya kawo karshen shekara tara da ya shafe a Spain.
Kungiyoyin biyu sun amince kan dan kwallon mai shekara 33 ya koma Italiya kan fan miliyan 105.

Hakan na nufin zai zamo daya daga cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.
Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.

Juventus ta bayyana cewa dan kwallo zai sanya hannu kan kwantiragin shekara hudu, sannan ta wallafa zanen dan wasan a sanfurin irin murnar da yake yi idan ya ci kwallo:
"Lokaci ya yi da zan bude wani sabon shafi a rayuwata, a don haka na nemi kulob din ya sayar da ni", kamar yadda ya fada a wata sanarwa da aka fitar .

Paris St-Germain ne suka sayi 'yan wasa biyu mafiya tsada a duniya - fan miliyan 200 ga Barcelona domin sayen Neyrmar, da kuma miliyan 166 don sayen dan Faransa Kylian Mbappe a watan Yuli bayan ya shafe shekara daya a matsayin aro.

Barcelona ma ta biya Liverpool fan miliyan 142 lokacin da ta sayi Philippe Coutinho a watan Janairu.

Rahoto:- bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: