Saturday, 14 July 2018
Burina Nayi Fice Fiye Da Davido Da Wizkid A Fagen Waka- Aminu Real Boy

Home Burina Nayi Fice Fiye Da Davido Da Wizkid A Fagen Waka- Aminu Real Boy
Ku Tura A Social Media
Ismail Aminu wanda aka fi sani da ‘Real Boy’, Karamin Yaro ne Dan kasa da shekara goma 11 haihuwa, wanda ya hore ma basirar iya wakar zamani, wanda a turance ake kira da Hip Hop, kuma an haife shi a shekarar 2007, a Karamar hukumar Kaduna ta Arewa, da ke Jihar Kaduna.

Ismail Aminu (Real Boy), ya yi fice sosai a fannin rubuta wakokin Turanci da Hausa zamani wato Hip Hop, sannan ya shara wajen iya yin rawa fiye da yadda ake zato. A halin yanzu ya sami nasarar raira wakoki masu tarin yawa a karkashin Kungiyar Matasan nan da ake kira Dynamic Arewa Empire, dake kaduna.

Masana masu yin sharhi akan Al’amuran da ya shafi rawa da waka, sun bayyana Ismail Aminu (Real Boy) a matsayin Matashin mawakin da a halin yanzu tauraronsa ke haskawa tun bayan rasuwar hazikin mawakin nan Lil Ameer, dake Jihar Kano, domin a cewarsu, a halin yanzu Manya da Kananan Mawaka na ta hadakar zawarcin Yaron domin ganin sun yi waka a tare da shi.

A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, Ismail Aminu (Real Boy), ya bayyana ma wakilinmu cewa, burinsa shi ne ya ga cewa ya daukaka a fage waka fiye da mawakan nan na Kudancin kasar nan, wato Wizkid ko Dabido. Sannan ya kara da bayyana cewa, babban burinsa a rayuwarsa bai wuce a ko da yaushe ya ga yana taimaka ma marasa galihu da kuma marayu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: