Sunday, 15 July 2018
Ba Mu Yarda A Kirkiri 'Yan Sandan Jihohi Ba, Kuma Ba Mu Amince A Hana Fulani Kiwo A Wasu Jihohi Ba, Cewar Sheik Sani Jingir

Home Ba Mu Yarda A Kirkiri 'Yan Sandan Jihohi Ba, Kuma Ba Mu Amince A Hana Fulani Kiwo A Wasu Jihohi Ba, Cewar Sheik Sani Jingir
Ku Tura A Social Media


ASh-Shehk Muhammad Sani Yahaya Jingir, shugaban Malamai na kasa na kungiyar Izala ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya tun daga fadar shugaban kasa zuwa ga 'yan majalisu akan 'yan sandan jihohi da kuma batun hana Fulani kiwo a wasu jihohi.

Sheik Sani Jingir ya bayyana hakan ne a jiya a yayin hudubar sallar Juma'a a masallacin 'Yan Taya dake garin Jos.

Shehk Jingir ya ce bai yarda da kirkiro 'yan sandan jihohi ba kuma bai yarda da hana Fulani kiwo ba a jihohin Taraba da Benua. Ya ce wanna zalunci ne da rashin adalci.

Shehin Malamin ya kara da cewa wasu Gwmnoni sun yi amfani da 'yan sandan gwamnatin taraiya sun kashe al'umar musulmi bare a ce an ba su damar kirkirar nasu. To an jefa kasa a cikin matsala kenan.

"Dan haka bama goyon bayan haka, Kuma bamuyarda ayiba yan majalisu mu da muka zaba kun ji ra'ayinmu", inji Sheik Jingir.

Daga Alhassan Adam Dangata
Jibwis Social Media

Share this


Author: verified_user

0 Comments: