Friday, 29 June 2018
WATA SABUWA. Zamu yi wa Dr. Ahamed Gumi raddi, kuma zamu zakulo karerayin da ya ke wa al'umma-Musa Yusuf Asadussunah.

Home WATA SABUWA. Zamu yi wa Dr. Ahamed Gumi raddi, kuma zamu zakulo karerayin da ya ke wa al'umma-Musa Yusuf Asadussunah.
Ku Tura A Social Media


Daga Datti Assalafy 

Muna anfani da wannan damar wajen sanar da 'yan uwa musulmin duniya cewa Bijimin matashin malamin sunnah Ash-sheikh Musa Yusuf Asadussunnah Kaduna (H) zai gabatar da mashahuriyar Lecture mai taken MUFTI KO MUFSIDI, MAI FATAWA NA 'KASA KO MAI 'BARNA NA 'KASA wannan lecture raddi ne ga Dr. Ahmad Gummi.

Kuma lecture ne da za'a warwarewa musulmin Nigeria da duniya gabaki daya dukkan wasu miyagun akidu da 'karya da gubar da Likitan Kaduna Dr. Ahmad Gummi yake fesawa a tsakanin al'ummar musulmin Nigeria

Insha Allahu Malam zai gabatar da karatun ranar Asabar 15 ga watan Shauwal Hijirar Annabi (saw) 1439 wanda yayi daidai 29/6/2018, za'a gabatar da Karatun a Masallacin Ahlul Baiti Wassahaba dake Hausawa Road Tudun Wada Kaduna State Nigeria daga misalin karfe 8:00pm na dare zuwa 10:00pm

Wadanda suke da zama a garin Kaduna don Allah kada ku bari a baku labarin wannan mashahuriyar Lecture, kuyi cincirindo kuje ku saurara, domin Malam ya shirya ma Lecture din! Allah Ya baku ikon zuwa Amin.
Wadanda suke tare damu a group whatsapp ku shirya insha Allah zan daura karatun da zaran Malam Ya kammala.

Malam Musa Yusuf Asadussunnah ya kirani a waya yace insha Allahu daga yanzu Malam Datti mun shirya zamubi mataki daki daki wajen mayar da martani ga Dr. Ahmad Gumi, kuma Malam yace min kafin ya gabatar da karatun zai kira ya sanar dani domin mu yiwa al'ummar musulmi albishir

Muna rokon Allah Ya tsare al'ummar musulmi daga sharrin da Dr. Ahmad Gumi yake yadawa, muna masa fatan shiriya da dawowa kan tafarki na gaskiya
Allah Ka zama jagora ga Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah Ka kara masa hazaka da zalaka da ilmi mai albarka

Share this


Author: verified_user

0 Comments: