Friday, 22 June 2018
To fah ! Miyasa Hadiza Gabon Ke Tonon Sililli A Shafinta Na Istagram Karanta

Home To fah ! Miyasa Hadiza Gabon Ke Tonon Sililli A Shafinta Na Istagram Karanta
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta yi wa wadanda "take bi bashi" dirar mikiya a shafin sada zumunta na Instagram, inda take kira gare su da su biya basussukan da take bin su.

A ranar Alhamis ne jarumar ta dinga wallafa sakonni na shagube ga wadanda ta ce ta na bi bashi, amma ba ta ambaci sunayensu ba.
A sakon farko da ta wallafa dai ta ce "A dinga biyan bashi Wallahi zan kira sunayenku."

BBC ta tuntubi Hadiza, don jin ko me ya sa ta dauki matakin aike wa da wannan sako a shafin sada zumunta maimakon ta gaya musu a sirrance, sai ta ce: "Ba zan ce komai ba kan wannan."

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin jarumar na cewa tana bin bashi, amma dai wasu masu shirya fina-finai kan nemi jarumai su yi musu fim ba tare da sun biya su hakkinsu lakadan ba.


Da aka tambaye ta ko nawa ne jumullar kudaden da take bi bashin, da kuma sunayen wadanda take bi, nan ma sai ta kara cewa: "Ni fa ba zan kara cewa komai ba, amma dai nan gaba kadan zan wallafa sunayensu a Instagram."

A sakonnin da ta wallafa din dai, Hadiza ta nuna cewa ta na bin wasu mutum hudu bashin na naira miliyan 2.8 da naira 350,000 da naira 75,000 da kuma naira 30,000.
Ta kuma wallafa cewa wanda take bi 30,000 din cikon kudin aiki ne da ta yi ba a biya ta ba.
Ta kuma yi ta nanata cewa kar a ce za a bata hakuri kan batun kuma kar a tura mata sakon rarrashi ta manhajar Whatsapp ko Instagram.

Mutane da dama dai sun yi ta tsokaci kan sakonnin nata, kuma mafi yawansu sun dinga nuna mata cewa lallai ta yi duk bakin kokarinta don ganin an biya ta kudinta.
Kadan ne daga cikin mabiyan nata suka yi tsokacin da ke rarrashinta ko kuma ta bata hakuri.

Hadiza Gabon na daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fagen fina-finan Kannywood, kuma ita ce ta biyu cikin wadanda suka fi dumbin mabiya a shafin Instagram.
Mutum 735,000 ne ke bin ta a shafin Instagram kawo yanzu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: