Monday, 4 June 2018
Tashin hankali : Ni Ba Milyan 100 Na Baiwa Dauda Rarara Ba Milyan 180 Na Bashi Kuma Ba Mawaka Kadai Keda Kudaden Ba Harda YAN-FIM- inji Abdulazeez Yari

Home Tashin hankali : Ni Ba Milyan 100 Na Baiwa Dauda Rarara Ba Milyan 180 Na Bashi Kuma Ba Mawaka Kadai Keda Kudaden Ba Harda YAN-FIM- inji Abdulazeez Yari
Ku Tura A Social Media
 Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari yace shi ba nera Milyan Dari 100 ya baiwa mawaki Dauda Kahutu Rarara ba nera Milyan Dari da tamanin 180 ya bashi, kuma ba mawaka kadai keda kudaden ba harda Yan-fim din Hausa wato Kannywood. 

Matemakin Shugaban kungiyar mawakan Ibrahim Yala Shiya bayyanawa wakilin Jaridar Dimokuradiyya Shuaibu Abdullahi, ta wayar tarho yace sun hadu da AbdulAziz Yari a dakin Allah dake birnin makka kasa mai tsarki jiya yake tabbatar mishi da haka.

Ibrahim Yala yace Abdulaziz Yari da kanshi yace mishi shi nera Milyan 180 ya baiwa Dauda Rarara ba nera milyan dari ba kuma bashi ya bayar da kudaden a aljihun shi ba kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC ne daga asusunta ta bayar da kudade.

Jaridar Dimokuradiyya ta wallafa cewar AbdulAziz Yari yace Kuma ba kungiyar mawaka aka baiwa kudaden su kadai ba harda Yan-fim din Hausa, kan irin gudunmawar da suka bayar.

Saboda haka Gwamna Yari yace tunda korafe korafe yayi yawa bari idan ya dawo daga Umara zai shirya taro ya gayyaci kowa yayi bayani a gaban su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: