Tuesday, 26 June 2018
Shugaba Buhari Ya Umarci Sauya Jami'an 'Yan Sandan Jihar Zamfara.

Home Shugaba Buhari Ya Umarci Sauya Jami'an 'Yan Sandan Jihar Zamfara.
Ku Tura A Social Media

A kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci sauya jami'an yan sandan dake jihar Zamfara domin dakile ayyukan ta'addancin da barayin shanu ke haddasawa.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne jiya a fadar mulki ta Aso Rock dake birnin tarayya Abuja yayin da yake ganawa da tawagar 'Supreme Council for Sharia in Nigeria'. Shugaban ya kara da cewar, yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya shawo kan matsalolin tsaron jihar Zamfara da sauran sassan kasarnan. 

Buhari ya cigaba da cewar, sakamakon rashin gamsuwa da kokarin jami'an yan sanda a jihar Zamfara, ya yi umurnin sauya manyan jami'an yan sanda na jihar da kuma kananan yan sandan da suka kai shekaru uku suna aiki a jihar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: