Sunday, 10 June 2018
Sau Biyu Buhari Na Aiko Min Da Takarda Inje Mu Gana Naki Zuwa domin Rashin Sakin Zakzaky-- Inji Sheik Dahiru Bauchi

Home Sau Biyu Buhari Na Aiko Min Da Takarda Inje Mu Gana Naki Zuwa domin Rashin Sakin Zakzaky-- Inji Sheik Dahiru Bauchi
Ku Tura A Social Media

Daga M.Inuwa Mh

Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya. Shehu Dahiru Bauchi, ya ce.

 Tun daga lokacin da Buhari ya hau mulki sau biyu yana aiko min da takardar gayyata a kan in je mu gana amma naki zuwa.

Lokacin da ya aiko min ta farko na fada masa ba zan je inda yake ba matukar bai saki Malam Ibrahim Elzakzaky ba, saboda abinda aka aikata a kan sa da almajiransa maras imani ne kadai zai ji dadin irin yadda aka kashe su maza da mata da yaransu.

Bayan nan ya sake aiko min da takarda a shekarar da ta gabata ta 2017 nan ma ban saurareta ba har kirana ya yi ta wayar tarho, amma nace masa ba zan yarda mu gana ba sai ya saki zakzaky. "In ji shehun malamin kamar yadda ya bayyana a lokacin da almajiran Malam Elzakzaky, suka kai masa ziyarar barka da shan ruwa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: