Wednesday, 20 June 2018
Nasara Ce Ta Sa Mu Shirya ‘In Search Of The King’ – Jammaje

Home Nasara Ce Ta Sa Mu Shirya ‘In Search Of The King’ – Jammaje
Ku Tura A Social Media
Masu magana dai su kan ce na ji dadi shi ne gari ba na saba ba, kuma wajen da dariyar makaho ta karbu, to a nan ya ke ajiye sandarsa. Da alama dai hakan ce ta faru ga fitaccen malamin Turancin nan, KABIRU MUSA JAMMAJE, domin kuwa kusan shekaru biyu da suka wuce ne ya yi wa masana’atar finafinai ta Kannywood wata shigar bazata a matsayin furodusa kuma ya shiga da wani salo na labarin da ba a saba da irinsa ba a masana’antar. Sannan wani abu da ya fi muhimmanci shi ne yadda ya shiga da salon din fim harshen Turanci kuma da ya ke ya shigo a sa’a tuni ya samu karbuwa a wajen masu kallo, domin kuwa a yanzu ya shirya finafinai har guda uku da harshen Turanci, wato This is The Way, Light and Darkness da There’s A Way. Kuma This Is The Way da Light and Darkness sun shiga kasuwa, yanzu a na jiran fitowar There’s A Way ne.

Sai dai kuma a yanzu Kabiru Jammaje ya dukufa kan aikin wani sabon fim mai suna ‘In Search of the King’. Don haka ne wakilin
LEADERSHIP A YAU LAHADI, RABIU ALI INDABAWA , ya ji ta bakinsa a game da salon da ya ke bi na shirya finafinai da Turanci a Kannywood da kuma irin nasarorin da ya samu. Ku biyo mu ku ji yadda ta kasance:
Malam Kabiru Jammaje ka shirya finafinai har guda uku na Turanci, biyu sun shiga kasuwa, daya kuma ya na kan hanya. Ko ya ya ka kali tasirinsu a wajen masu kallo?
To, ka san fim din da mu ka fara yi na farko This is the Way ya yi nasara, domin ko a gidan rediyon BBC sharhinsu kan finafinai da su ka yi fice a 2016 shi ne a sahun farko. Wannan ya ba mu karfin gwiwar da muka yi na biyu, wato Light and Darkness, sakamakon irin karbuwar da muka ga ya yi wanda har ya samu cin gasar finafinai ta Arewa, wato Amma Award, kuma shi ma Light and Darkness mun shiga gasar wannan shekara da shi inda shi ma ya samu nasara a wurare da dama, shi kuma na ukun This Is The Way, kamar yada aka sani ci gaba na farko ne kuma duk da dai bai fito kasuwa ba an nuna shi a sinima a Colom Waya Dosamnar da ya gabata zuwa farkon wannan shekarar, kuma na san masu kallo suna nan suna ta jiran fitowarsa kasuwa a gidajen TB. To amma da yardar Allah zai fito nan gaba adan, dama al’adar kamfaninmu Jammaje Production ba ma sakin fim sai mun yi wani sabo sai mu saki wani kuma a yanzu mun fara shirin yin wani fim zuwa bayan slalar nan idan Allah ya yarda za mu fara aikin sabon fim din mu mai suna “In Searh of the King” wanda yake sabon labari ne da ya shafi sarauta da kuma al’ada musamman a masarauta a kasar Hausa. To, idan muka gama za mu saka tallar a cikin fim din da za mu fitar do haka dai masu jiran fim din su yi hakuri ya kusa fitowa.
Sai dai a na ganin kamar tsawon lokaci da fim din ya dauka bai fito ba hakan zai sa mutane su manta da shi.
To, ba ma fata hakan kuma da yardar Allah ba za su manta ba, domin kuwa shi There’s a Way fim daya ne tamkar da goma kuma ka san fiafinan Turanci a Kannywood kamfanin mu ne kadai yake yi don haka babu wannan gasar, don haka mutane ba za su manta ba, kuma mun yi shi mai inganci a cikin tsarin da ya dace.

Finafinanka na farko sun shafi rayuwar matasa ne da zamantakewarsu musamman ta fannin karatu, yanzu kuma sai aka ga ka juya zuwa ga bangaren Sarauta da al’ada. Ko me ya ja ra’ayinka?

To, abinda ya ja ra’ayina dai shine, fim din da muka fara yi a baya This is the Way da kuma Light and Darkness na je kasar ingila mun zauna da wasu Turawa sai na nuna musu fim din kuma haka ya haifar da tattaunawa a tsaaninmu. Suke tambaya ta cewa su wadannan da suke cikin fim din su wane ne a ina suke? Sai nake ba su amsa cewar a Afirka suke a kasar Nigeria kuma a yankin Arewa. Har muka rinka tattaunawa a kan yanayin fim din da kayan da jaruman suka yi amfani da shi. To sai na ga abin ya burge su. Don haka bayan na dawo gida suka rinka kira na suna tambaya ta ina ci gaban fim din yake. Sannan Malam Muhsin Ibrahim wani mai sharhi a kan finafinai a kasar Jamus yake da zama ya nuna wa dalibansa da suke an fim din kuma sun rinka yin tambayoyi a kan fim din. To dai duk wanda ya kalli fim din yana son ya kali ci gabansa. To wannan ya s ana ga cewar lallai akwai bukatar mu yi fim na al’ada. Kuma karin dalilin bayan na je birnin London na shiga wata sinima sia na ga wani dan kasar Tanzania ya kai fim dinsa kuma idan ka kalli fim din ta fuskar ci gaba, to gaskiya bai kai na Turawa ba, amma yana da labari mai kyau yana ba da labarin mutanen Afrika da al’adarsu. To, wannan ne ya sa suka karbi fim din har suka nuna shi a sinima a London. Don haka wadannan abubuwa suka karfafa mn gwiwa na ga cewar mu ma akwai bukatar mu zo da wani fim na al’ada wanda ba kawai zamantakewar mutanen Arewacin Nigeria na yanzu zai nuna ba, zai tabo al’ada, Sarauta da sauransu. Don haka ne muka samar da wani labari mai suna “In Search of the King.” Wanda shi ne a yanzu muke shirin yin sa. Shi labarin wani ne da yake tafiya neman wani sarki kuma abubuwa da dama suka faru a tafiyar tasa kuma na tabbatar dai idan aka gama fim din mutanen da suke kasar nan da ma na Turai fim din zai burge su. Don haka yanzu burina idan mun gama fim din bayan mun kalle shi a nan zan kai shi London a nuna shi kuma ina fatan su ma za su yi alfahari da shi.

An saba yin finafinai na al’ada a Kannywood ko irin salon da aka yi ka dauka wajen isar da sakonka?

To, gaskiya salon ba iri daya ba ne, shi ya bambanta da wanda aka saba gani kuma da yardar Allah sai ya canja alkiblar harkar fim ta Kannywood. Domin kuwa zama muka yi muka hada karfi da kafe don gudanar da aikin kuma marubucn labarin Aminu Sharif Ahlan sananne ne a harkar fim ya iya tsara labari mai kyau, duk da haka ba mu sakar masa ragamar ba tare da muka zauna muka yi aikin don haka na tabbatar labarin yana da bambanci da wanda aka saba gani kuma za mu kawo sabbin jarumai a ciki a yanzu muna sa ran za mu fara daukar fim din sati biyu bayan karamar Sallah.

To, a yanzu ganin lokaci yana karatowa, wanne irin shiri aka yi don ganin aikin ya samu nasara?

A yanzu dai shirin da muka yi mun fitar da kasafin aikin sannan kuma an gama tsara labarin har ma wasu jaruman sun fara samun guraben da za su fito, kuma mun yi magana da mafi yawan jaruman da za mu yi aikin da su, sai kuma wani abu da zai ba da mamaki shi ne, har mun saka ranar da za a nuna a shi a sinima wato a watan Disamba na karshen shekara, kuma ina so Jammaje Production su rike al’adar duk karshen shekara zuwa farkon sabuwar shekara za mu rinka nuna finafinan mu a sinima. Don haka ina yi wa mutane albishir da cewar, a wannan fim din da za mu yi mai suna In Search of the King, za a ga shi kansa turancin da muka yi amfani da shi ya kara samun inganci fiye da na baya. Don haka za a ga irin ci gaban da aka samu ta gannin kalmomin Turanci kuma mun samu kwararren Darakta Balarabe Murtala Baharua shi ne zai ba da umarni, kuma za a ga sabon jarumin fim din Abdullahi Amdaz ne duk da yake ba a san shi ba a matsayin fitaccen jarumi an fi sanin sa a matsayin marubucin labari. Wannan ne farkon da zai ja fim daga farko har karshe. Mun yiaka ne saboda mutane sun nuna mana jn dadinsu da ake kawo sabbin jarumai ba wadanda aka saba gani yau da kullum ba.


Ko mene ne sakonka na karshe?

To sakona na karshe dai shi ne sabon fim dn mu This is the Way yana nan fitowa kuma a cikinsa za a ga tallan In Search of the King. Kuma muna fatan idan ya fito mutane su nemi kwafi mai kyau su saya kada su sayi wanda aka yi mana satar fasaha. Sannan In Search of the King za a nuna shi a sinima a karshen wannan shekarar zuwa farkon sabuwar shekara.

Sources:leadershipayau.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: