Friday, 29 June 2018
Kalli kyawawan Hotunan Bukin Auren Meram Indimi Na Shagalin Buki

Home Kalli kyawawan Hotunan Bukin Auren Meram Indimi Na Shagalin Buki
Ku Tura A Social Media

Garin Maiduguri na jihar Borno ta samu manyan baki sakamakon bikin auren yaran attajiri dan kasuwa, Muhammed Indimi.
Diyar sa mai suna, Hauwa Indimi zata zama amaryar Muhammad Yar'adua, dan tsohon shugaban kamfanin NNPC.

Tun makon da ya gabata Hauwa da angonta mai jiran gado suka fitar da hotunan kafin auren su wanda ya yadu a duniyar gizo.

Haka zalika ita ma Meram Indimi zata shiga dakin aure bayan daura auren ta ga Baffa Dandatti Abdulkadir.

Ranar 27 ga watan Yuni aka gudanar da biki gabanin ainihin ranar daura aure wanda zai gudana ranar juma'a ga wata duk a nan masallcin Indimi dake jihar Borno.

Labarin auren su da hotunan shagulgulan biki ya mamaye kafaffen watsa labarai na yanar gizo kamar yadda akasari ake zato zai faru.

Iren-iren bikin auren ya kan samu halartar manyan yan kasa da ma yan kasar waje masu hannu da shuni a ma'aikata daban.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: