Monday, 4 June 2018
Ina Matukar Takaici Da Wasu Bata Ke Amfani da sunana wajen Damfara - Maryam Booth

Home Ina Matukar Takaici Da Wasu Bata Ke Amfani da sunana wajen Damfara - Maryam Booth
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jaruma Maryam Booth tayi gargadi ga masoyan ta da masu bibiyan shafin ta da su kauraci shafukan bogi da ake budewa da sunan ta.
Maryam ta nuna bacin ran ta ga masu damfara wadanda suke amfani da sunan ta wajen karbar kudin jama'a.

Daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa a kwarya shine yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a ta hanyar da wasu bata gari keyi.
Ban da haka jaruman suna kara fuskanta barazanar daga masu satar bayanar sirri ta hanyar konfuta.

A hallin yanzu dai jaruman sun tsaurar matakin kan wadanan matsaloli da suke fuskanta kuma Maryam ta gano matakin da suke bi wajen yin damfara.

A sakon da ta wallafa a shafin ta tare da bayyana hoton shafin da aka bude da sunan ta, jarumar tayi kira ga jama'a da su sani cewa ita bata taba neman bukatar kudi daga masoyan ta domin sanin kowa ne cewa ita tana gudanar da harkar kasuwanci.

Tayi fashin baki inda ta zagi masu aikata ire-iren harkar damfara kuma ta jingina bakar ta albakarcin wannan watan Ramadan da ake ciki.

Tana mai cewa duk wanda aka kama mai aikata wannan laifin ya sani cewa ba za'a takaita matakin hukunci ba.

Daga karshe tayi Allah-wadai ga masu baiwa mutane kudi ba tare da sun tabbatar da sahihancin wanda ke neman bukatar. "Sai kace wanda ke da tabin hankali"? ta mai bayana cewa ita dai bata taba nemi bukatar masoyan ta ba alhali tana kasuwanci.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: