Friday, 15 June 2018
Hauwa Maina Bayan Wata Daya Da Rasuwa, fitacciya Jaruma Ta Samu Jika

Home Hauwa Maina Bayan Wata Daya Da Rasuwa, fitacciya Jaruma Ta Samu Jika
Ku Tura A Social Media

Maryam Bukar Hassan ta haihu ne a daren ranar talata 12 ga watan Yuni a garin Kaduna bayan ta dawo gidan kakar ta inda take karban gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta.

Diyar fitacciyar jaruma Hauwa Maina ta samar mata jika bayan wata daya da rasuwar ta.
Maryam Bukar Hassan ta haihu ne a daren ranar talata 12 ga watan Yuni a garin Kaduna bayan ta dawo gidan kakar ta inda take karban gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta.

Rahotannin sun bayyana cewa diyar ta dawo kaduna ne daga gidan mijin ta dake garin Abuja bayan rasuwar babbar ta.Mariganya ta rasu ne a ranar 2 ga watan Mayu  bayan wata rashin lafiya da tayi. Rasuwar ta ya girgiza jama'a da dama a arewa musamman ma abokan aikin ta a masana'antar fim ta kannywood.

Kamar yadda diyar ta wallafa a shafin ta don sanar da farin cikin ta da samun karuwar, Maryam wacce aka fi sani da Alhanislam a Instagram  ta bayyana farin cikin ta bisa ga karuwar da tayi ta kara da cewa mahaifiyar ta so tayi ma jikan ta tozali sai dai kuma ajali ya riske ta.Welcome o my beloved baby boy, born on 27th Ramadan ...officially "umm ramadan"💘💘💘 a.k.a Alhanislam,grandma wanted seeing u badly man,but Allah had other plans,she left and u came,indeed with pain comes ease,she was a heartbreak I concealed ,I died from within,but u my love is a beautiful remedy ....and I remember when I wrote this for you,couple of months ago... .......................................................................................... ........................................................................................................................................................................................ It hurts just seating here calculating how many more vomits i have to go ,before seeing your glorious face, And how many sores that could cause in my throat, It hurts cause I wish u were already here to dry my tears of pain ... The changes my body's going through to make sure u make it to the world, How sleepy I get but can't find the sleep sometimes cos of the discomfort I feel How my knees snaps sometimes and my legs shake How my back and head aches And how sometimes my vision is affected ... But its all worth it as I think of holding u in my arms my beloved one... I hope u remember all this and also remember that at whatever age u might be ,through it all,u wouldn't have to carry any pain by yourself , that's what am meant for ,let me carry all your pains and burdens ...May u be happy all your life my child❤
A post shared by maryam Bukar (mrs umar Zuruq ) (@alhanislam) on
Maijegon ta bayyana wannan haihuwa a matsayin wani babban abin farin ciki da ya same ta a daidai lokacin da ta ke cikin jin zafin rabuwa da mahaifiyar ta.

Kwanaki baya Maryam wacce alakar ta da mahaifiyar ta baya boyewa ta bayyana cewa zata cigaba da amfani da shafin mariganya wajen yin da'awa.

Gabanin rasuwar ta, Hauwa Maina, ta kasance daya daga cikin kashin baya da suka raya masana'antar fim tun ranar da aka kafa ta.

Tayi fice wajen fitowa a matsayin jarumar shiri da kuma shirya fim da kanta tare da bada umarni.

Tayi suna sosai bisa yanayin rawar da take takawa a fim a matsayin uwa ko mai tausayi.

Muna mata Addua, Allah ya jikanta da Rahama. Ita kuma mai jego Allah ya raya kuma Allah ya kara mata lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: