Wednesday, 6 June 2018
Dalilin Da Yasa Nake Saka Irin Kayan Da Nake Sakawa a Wakokina – Adam A Zango

Home Dalilin Da Yasa Nake Saka Irin Kayan Da Nake Sakawa a Wakokina – Adam A Zango
Ku Tura A Social Media
Shahararren jarumin nan na kannywood kuma mawaki, Adam A.Zango yayi Magana akan korafin da jama'a keyi game da irin kayan da yake sanyawa a cikin bidiyon wakokin shi. 


A wata hira ta musamman wanda ya wallafa a shafin sa na zumunta, Zango ya bayyana cewa ya na sanya irin kayan zamanin ne domin janyo hankalin jama'a wajen kallon wakokin yan arewa. 
Yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi. 


Ya kara da cewa mafi yawanci mabiyan sa masu bibiyan wakokin turawa da na india basu san kalamai da mawakan ke furtawa a cikin wakokin su kuma mafi yawanci kalamai ne wanda bata dace ba wanda bahaushe kuma musulmi ya dinga furtawa. 


cewar sa yana kokari wajen rera wakoki cikin yaren hausa kuma ya sanya mata kida irin ta zamani kuma ya sanya kayan zamani a cikin ta domin janye hankalin jama'a zuwa kallon nashi.

 Najeriya Ya jadadda cewa hakan yunkuri ne na janyo hankulan mutanen arewacin kasar wajen yin alfahari da mawakan yankinsu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: