Saturday, 30 June 2018
Da Farawa Da Iyawa : Wata 'Yar Saudiyya Ta Saki sabuwar Wakar Rap Tana Tuki

Home Da Farawa Da Iyawa : Wata 'Yar Saudiyya Ta Saki sabuwar Wakar Rap Tana Tuki
Ku Tura A Social Media


Kasa da mako daya ne mata suka samu'yancin tuki a Saudiyya, kuma ba tare da bata lokaci ba har wata mawakiya ta saki sabuwar waka tana tuki.
Bidiyon sabuwar wakar rap da larabci da mawakiyar mai suna Leesa A ta saki, ya ja hankali a shafukan sada zumunta na intanet.
Ta saki bidiyon ne da take waka tuna tuki a ranar da wa'adin dage haramcin tuki ga matan Saudiyya ya kawo karshe.
An nuna mawakiyar tana zaune a kujerar direba rike da sitiyarin mota kirar Hyundai, kuma a cikin baitukan wakar ta ce "Ba na bukatar kowa ya dauke... ina da lasisin tuki"
Kadin dage haramcin a ranar 24 ga watan Yuni, mata ba su da 'yancin tuki, inda sai dai a yi hayar direba ya dauke su.
Hotunan yadda matan Saudiyya ke murnar fara tukin mota
Haramcin tuki ga mata ya kawo karshe a Saudiyya
A farkon watan Yunin bana ne aka fara ba mata lasisin tuki bayan sanar da matakin dage haramcin a watan Satumban bara.
A baya dai mawakiyar Leesa A mabiyanta ba su da wani yawa a shafukan sada zumunta, amma sama da miliyan daya da rabi suka kalli bidiyon da ta wallafa a shafukanta na Instagram da YouTube.Bidiyon ya nuna tana tuki, tana taka totur da canza giya, kuma tana wakar rap.
"Yo kun manta ranar yau 10 ga wata, wannan na nufin babu tasi", wato tana nufin ranar watan musulunci da ta zo daidai da ranar 24 ga Yuni watan turawa.
A cikin waken ta ce "Ba wasa nake ba, yau zan yi tuki da kai na. Sitiyarin mota a hannaye na, totur da birki da kuloci duka a kafa ta".
Bidiyon wakar a twitter ya samu masoya kusan 9.5Million, kuma sama da 104, 000 suka aika da bidiyon a shafukansu.


Matan Saudiyya da dama sun yi matukar murnar kawo karshen haramta ma su tukin mota bayan shekaru da dama, inda bidiyo da hotunan yadda matan suka fara tuki suka mamaye shafukan sada zumunta.
Kafin dage haramcin, Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin tuki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: