Thursday, 7 June 2018
Bayan Sallah Gwamnan Zamfara Zai Tsare Rarara Kan Yayi Bayanin Inda Ya Kai Kudaden Mawaka Nera Milyan 180M

Home Bayan Sallah Gwamnan Zamfara Zai Tsare Rarara Kan Yayi Bayanin Inda Ya Kai Kudaden Mawaka Nera Milyan 180M
Ku Tura A Social Media

 Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari yasha alwashin gayyatar kungiyar mawaka da Yan'fim ciki harda Dauda kahutu Rarara domin yayi musu cikakken bayanin inda ya kai nera milyan 180.

Abdulaziz Yari wanda yanzu haka yana kasa mai tsarki domin gudanar da Umarah.

Hakan ya biyo bayan korafe-korafe da zarge-zargen dake yawo a kasar nan kan kyautar kudade da yawan su ya kai nera milyan 180 da kingiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC suka baiwa kungiyar mawaka da Yan-fim tallafi.

Kafin wannan lokacin su mawakan Dauda ya nuna cewar ba'a bashi ko kwabo ba, daga baya kuma yace nera milyan 60 aka bashi amma ya baiwa wadanda suka yi hanya kudaden suka fito nera milyan 18, ragowar milyan 42 kuma suna banki kuma akawut din shi ya sami matsala.

Baya ga haka sai Matemakin kungiyar Ibrahim Yala suka hadu a Gwamnan Zamfara a makka sai Gwamna ya tabbatar mishi da cewar shi ba nera milyan 60 ya biwa Dauda Rarara ba, nera milyan 180 ya bashi kuma bai baiwa kowa sile-biyar ba kuma ba mawaka kadai keda mallakin kudaden ba harda Yan-fim a cikin lissafin kudaden.

Yanzu haka dai Gwamna Abdulaziz Yari yasha alwashin bayyanawa mutane cikakken bayanin abunda ya faru a tsakanin shi da Dauda Rarara zuwa bayan Sallah.


Sources:JARIDAR DIMOKURADIYYA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: