Monday, 25 June 2018
Akwai Yiyuwar Mikel Obi Ya buga wasa Da Argentina Saboda Rauni

Home Akwai Yiyuwar Mikel Obi Ya buga wasa Da Argentina Saboda Rauni
Ku Tura A Social Media
Tawagar Likitocin Super Eagles da ke wakiltan Najeriya a gasar cin kofin duniya a Rasha na aiki ba-dare-ba-rana donin ganin Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar buga wasan da Najeriya za ta yi da Argentina a gobe Talata.
Binciken likitocin ya nuna cewa, dan wasan ya samu rauni a wuyar hannunsa a dai dai lokacin da ake dab da tashi wasan da Najeriya ta casa Iceland da ci 2-0 a ranar jumm’ar da ta gabata.

Koda dai Kocin Super Eagles, Gernot Rohr na kallon runin a matsayin karami wanda kuma ba zai hana Obi buga wasan da Argentina ba.
Rohr ya kuma bukaci ‘yan wasan nasa da su rika dukan kwallo da zaran sun hangi wata kafa a dab da ragar Argentina.

Rohr ya ce, wasan na gobe ba zai kasance mai sauki ba, kuma za su yi fafatawar ce da burin samun nasara amma ba canjaras ba kamar yadda wasu ke akalla fata.
Masharhanta kan harkokin wasanni na kallon wasan a matsayin mai zafi kwarai, lura da cewa Argentina na neman nasara ruwa a jallo don tsallakawa matakin gaba, yayin da ita ma Najeriya za ta yi kokarin samun karin maki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: