Wednesday, 6 June 2018
ABUN NEMA YA SAMU : Kungiyar "Mu'assasatul Anwarul Darikar Tijjaniya" Mai Shelkwata A Bauchi, Nigeria Ta Gayyaci Mukabala Ga Sheikh Kabiru haruna Gombe

Home ABUN NEMA YA SAMU : Kungiyar "Mu'assasatul Anwarul Darikar Tijjaniya" Mai Shelkwata A Bauchi, Nigeria Ta Gayyaci Mukabala Ga Sheikh Kabiru haruna Gombe
Ku Tura A Social Media

Daga Babangida A. Maina

Kungiyar "Mu'assasatul Anwarul Darikar Tijjaniya" Mai Shelkwata A Bauchi, Nigeria.

Ta Mika Goron Gayyatar Tattaunawa (mukabala) Ga Secretery Na Kungiyar Izala Ta Kasa,  (Kaduna) Sheikh Kabiru Gombe, Biyo Bayan Wani Ikrari Da Yayi Jiya 5/6/2018 a Wajan Tafsiri Dinsa Da Yake Gabatarwa a Masallachin 'Yan Lilo Dake "Tudun Wada Kaduna", Na Cewa Da Yayi Duk Wani Wanda Zai Iya Tamka Masa Akan Da'awar Da Yake Yi Akan Sufaye To a Shirye Yake, Yana Da Cocila Da Zai Haskashi.

Ana Saran Idan Ya Amsa, Muqabalar Zatafi Mai Da Hankali Akan,

1-- Tawassali Da ANNABI MUHAMMADU (SAW)
Da Sauran Bayin Allah Nagari Salihai (waliyyai).

2--- Ingancin Yiwa Annabi Muhammadu (saw) Salati da Wata Sigar ko Rashin ingancin Hakan.!

3 --- shin Annabi Muhammdu Yasan Gaibu Ko Bai Sani Ba.?

Da Sauran Abubuwa Wadanda Akeda Sabanin Fahimta a Tsakanin Sufaye Da qungiyar Izala.
Fatan Mu Dai Allah Yasa Ya Amshi Wannan Goron Gayyatar Kamar Yadda Shiya Nema Dakan Sa. Ameeeeeeen.

Duk Da Wasu Daga Cikin Yayan Kungiyar Sukan Fada Mana Cewa Mu Rabu Dashi Suma Ba Dadin Kasance Dashi Suke Yiba Wannan Kungiyan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: