Tuesday, 15 May 2018
YAUSHE ALI DA ZANGO ZA SU DAINA GABA?

Home YAUSHE ALI DA ZANGO ZA SU DAINA GABA?
Ku Tura A Social Media

Koda yake, na ɗan kwana biyu ban yi magana game da gabar da ta ke tsakanin fitattun jaruman Finafinan Hausa ba wato, Ali Nuhu da Adam A. Zango. 
Ba ku ma so na ke na tsokano gabar ta dawo farko ba. Sai dai waɗannan jaruman ku san duniya ta shaida cewa basu magana da junan su, tun bayan wani saɓani da ya shiga tsakanin su a watan Disamba na shekarar da ta gabata, wanda abin kunya ne a ce har yanzu basu daidaita ba a matsayin su na 'yan uwa musulmai. Shin wai ko dai basu san illar da ke tattare da waɗanɗa suke gaba da junan su ba? Ko kuma sun sani suka take sani? Ko suna sane sai sun je wajen Allah sai ya yi masu hukuncin daidai da abin da suka aikata a duniya.

Wadansu bangaren na jaruman da magoya bayan su, sun ɗauki wani tsarin rayuwa na daban marar dadi wanda ya sha bamban da irin rayuwar da Alƙur'ani ya nuna. Daya daga cikin kurakuran da irin wadannan mutane masu raunin imani da alfahari, wadanda ba su damu da aikin yaɗa sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu kyau ba, shi ne yadda suka dauki rayuwar wannan duniya kawai ba ta wuce  mutum ya yi fim, ya samu ƙuɗi, ya yi aure, ya haifi ‘ya’ya ya rene su sannan ya tara abin duniya.

Amma inda kuskuren yake shine sun manta da babban dalilin zuwansu wannan duniya, da kin tafiyar da ni’imomin da Allah ya yi masu na fifita su da ya yi kan kowa a cikin masana'antar da suke samun na wake da shinkafa. Sun manta kwata-kwata suna so duniya ta ruɗesu daga ƙarshe kuma idan ba su sake ba dukkan su mota tana iya aje su a tasha kamar yadda ta ɗauko su. 
Muna kira gare ku a matsayin ku na 'yan uwan mu musulmai “Ku bi Allah da Manzonsa kuma kada ku yi jayayya a junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce Mutum biyu sallar su bai wuce kawunan su. Na farƙo nashayin giya, na biyu masu gaba da junan su. A wani hadisin Manzon Allah ya ƙara da cewa ana bude ƙofofin aljanna ranar alhamis da litanin. Amma an jinkirtawa  mutum biyu sai sun shirya (su ne Masu gaba da junan su)

Mun yi tunanin gabar taku ba mai daɗewa bace, sai ga shi har watan azumi yana shirin kamawa, amma ba ku shirin yafewa juna.

Sources :kwannywoodexclusive

Share this


Author: verified_user

0 Comments: