Friday, 11 May 2018
YADDA TA WAKANA: A Jihar Kano Wajen Jana'izar Khalifa Isyaka Rabi'u (A cikin hotuna)

Home YADDA TA WAKANA: A Jihar Kano Wajen Jana'izar Khalifa Isyaka Rabi'u (A cikin hotuna)
Ku Tura A Social Media


Daga Anas Saminu Ja'en

Cincirindon jama'a kenan a lokacin gudanar da Sallar jana'izar Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u yanzu haka a birnin Kano.Cikin mahalarta jana'izar ciki har da shugaban sojojin Najeriya na kasa Birgediya janar Tukur Yusuf Burutai tare da wasu daga cikin gwamnonin Najeriya da dama da, inda gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tarbe su, tare da manya manyan mutane daga ciki da wajan Kano ga kuma al'umma daga ko'ina a fadin kasar nan.

Inda a safiyar yau kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo bisa jagorancin gwamna Ganduje, kuma ya ziyarci fadar Mai Martaban Sarki Kano Malam Muhammadu Sanusi ll, Ita ma Uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhar bisa rakiyar Uwar gidan gwamnan Kano Hajiya Hafsat Ganduje, suka ziyarci gidan Marigayin domin yiwa iyalan sa gaisuwa wannan babban rashin da aka yi.

Muna addu'ar Allah ya jikansa da rahama yasa Aljanna makomar sa, tare da magabatan mu baki daya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: