Monday, 14 May 2018
Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe A cikin Hotunan

Home Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe A cikin Hotunan
Ku Tura A Social Media
Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe a bisa namijin kokarin da yake wajen ganin an tabbatar da Sunnah a wannan nahiya.
  Da yake nasa jawabin shugaba Kungiyar na reshen Al-Hikima Ustaz Basheer Mainasara yake cewa
Sheikh Kabiru Gombe mutun ne mai kokari da jajircewa wanda baya damuwa da haushin masu haushi wajen fadin gaskiya da kuma ganin an tabbatar da Sunnah da kuma aiki da ita.

Kungiyar ta kara yabawa malam irin yadda ya samarwa Mata incinsu a wannan nahiya, koda yaushe malam yana kokarin fahimtar da mata a binda ya shafi zaman Aure yadda zasu zauna mazajensu da yadda zasu bada tarbiya ga ƴaƴan su domin asamu nagartaciyar Al-ummah.

Daga karshe Shugaban yayi kira ga malam ya kara kokarin da yakeyi wajen kira ga matsa su daina shaye-Shaye domin yana gurbata Al-ummah da kuma rayuwar ɗan Adam gabaɗaya.

Mustapha Ambursa.Share this


Author: verified_user

0 Comments: