Thursday, 3 May 2018
Tsohuwar jarumar kannywood Rahama Hassan Ta Sanyawa Diyarta Suna "ISlam"

Home Tsohuwar jarumar kannywood Rahama Hassan Ta Sanyawa Diyarta Suna "ISlam"
Ku Tura A Social Media
A labarin da jaridar Rariya ta fitar, tsohuwar jarumar tayi ma jama'a godiya bisa addu'o'i da fatan alheri da suke mata sakamakon haihuwar da tayi.

A cewar ta "Ina kara godiya da irin fatan alkairi da addu'oi da na samu daga gareku, na gode sosai. Mun sanya ma Ya'rmu suna ISLAM".

Ta kara da "Allah kuma ya bar zumunci ya Albarkaci rayuwanmu baki daya.

Wannan shine yar fari da ta samu aurenta da mijinta, Alhaji Usman Sani El-kudan,  wanda aka daura cikin ranar 6 ga watan janairu 2017.

Tsohuwar jarumar ta taka rawar gani yayin da take fim kuma tauraron ta ya haska matuka. Tana daya daga cikin jarumai mata da suka raya masana'antar fina-finan hausa bisa irin salon fitowar ta a shirin fim da dama.

Rahama ta fito a fina-finai da dama masu kayatarwa, cikin su akwai ''Birnin Masoya', 'Dan Marayan Zaki' da 'Karangiya'.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: