Wednesday, 30 May 2018
Sheik Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 67 Da Soma Tafsiri

Home Sheik Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 67 Da Soma Tafsiri
Ku Tura A Social Media


... ya kuma cika shekaru 54 yana tafsirn Kur'ani da ka ba tare da duba Kur'ani ba

Daga Ismat Suleja

A bana Maulana Sheikh Dahir Usman Bauchi ya cika shekaru 67 yana gabatar da Tafsirin Kur'ani. Ya fara Tafsirin Kur'ani a watan Ramadan na  Shekarar 1951. Sannan kuma a bana Sheihin Malamin ya cika shekaru 54 yana gabatar da Tafsirin kur'ani da ka ba tare da duba takarda ba.

Kana kuma a bana ya cika shekaru 39 yana Tafsiri a Birnin Kaduna tare da yin sauka uku a mashahurin Tafsirin da duniyar Ilimin Tafsiri ta Sallama masa akai wato fassara Kur'ani da Kur'ani, fassara Kur'ani da Hadisin Manzon Allaah SallalLaHu AlaiHi Wa AliHi Was Sallam, fassara Kur'ani da maganganun Sahabai da Tabi'ai da magabatan Bayi na kwarai.

Alhamdulillahi, cikin yardar Allah a ranar 25 ga watan Ramadan, Maulana Sheikh Dahir Usman Bauchi zai maimaita saukar Kur'ani a tafsirin watan Ramadan karo na uku, bayan shekaru 12 da sauka da aka gabatar a shekarar 2006 a filin taro na Murtala Square dake birnin Kaduna.

Muna addu'a Allah Subhanahu Wa Ta'Allaah Ya sanya mu daga cikin wadanda za su halarci wannan taro na bana da za a yi a ranar 10 ga watan Yuni, 2018 a filin taro na Murtala Square dake Kaduna.

Muna Rokon Allaah Subhanahu Wa Ta'Allaah Ya ja mana kwanan Shehu, Allaah Ya kara masa, lafiya. Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: