Thursday, 31 May 2018
Sharuddan Da Saraki, Dogara Da Su Kwankwaso Suka Gindaya Domin Zama A APC

Home Sharuddan Da Saraki, Dogara Da Su Kwankwaso Suka Gindaya Domin Zama A APC
Ku Tura A Social Media

1. Daga cikin sharuddan da suka gindaya sun hada da janye kararrakin da aka shigar a kan shugaban majalisar dattawan kasar Abubakar Bukola Saraki.

2.  Bai wa Kakakin majalisar wakilan tarayya Yakubu Dogara da tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso damar samun gurabu a zaben share fage da jam’iyyar APC ta gudanar a jihohinsu.

3. Kawo karshen abinda suka kira tursasawa da hukumar yaki da rashawa EFCC ke yi wa wasu daga cikinsu.

4. Sannan kuma da jan kunne babban sufeton ‘yan sanda kasar sakamakon kin gurfana gaban majalisar dattawa duk da sammacin da aka tura masa.

Shugabannin gungun na sabuwar PDP wadanda suka bar tsohuwar jam’iyya mai mulki domin mara wa Muhammad Buhari a zaben shekara ta 2015, sun ce matukar aka kai karshen wannan wata na yuni ba tare da warware wadannan matsaloli ba, to ko shakka babu matsalar za ta iya yin tasiri ga yunkurin samar da hadin-kai tsakanin ‘yayan jam’iyyar APC kafin zaben shekara mai zuwa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: