Thursday, 10 May 2018
Sharhin Fim Din "Yusra"

Home › › Sharhin Fim Din "Yusra"

Post By:

Ku Tura A Social Media
09097438402 habibsaddika@gmail.com
Suna: Yusura
Tsara labari: Sulaiman Bello Easy
Producer: Kabiru A Yako
Bada umarni: Sulaiman Bello Easy
Kamfani: Gadon Kaya Multimedia tare da Dogon Yaro Mobietone
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Hadiza Muhammad, Rabi’u Rikadawa, Abdullahi Bankaura, Hajara Usman, Kabiru Yako, Hajara ‘yar Fillo tare da Yusura ‘yar Fulani
Sharhi: Saddika Habib Abba
A farkon fim din an nuna Yusura a dakinta tana barci sai wani kato ya shigo ya fara barazanar yi mata fyade a lokacin mijinta Alhaji Sa’idu (Rabi’u Rikadawa) tare da kishiyarta Hajiya Salma (Hadiza Muhammad) suka ji ihunta suka shigo cikin dakin suna shigowa sai katon ya sauya zuwa makirci sai ya kwanta akan gadon yana yi mata magana wadda kowa zai zaton tare suke shi da ita, Alhaji Sa’idu yana jin haka a gurin ya yi mata saki uku ta koma gidansu cikin bacin rai mahaifiyarta (Hajara Usman) ta fara yi matan fadan dama bin maza takeyi shiyasa taki yin aure da wuri? domin dama an nuna ansha fama kafin Yusura ta amince tayi aure duk saurayin da ya zo wajenta bata saurararsa, A haka har ta auri Alhaji Sa’idu abisa dalilin matarsa Hajiya Salma wadda ita kuma bata haihuwa gashi yana da tarin dukiya kasancewar kada tadauki hakkinsa yasa ta saka shi a dole ya auri Yusura domin ‘yar uwarta ce ma Yusuran.

Bayan wani lokaci mahaifiyar Yusura ta fuskanci cewar Yusura bata da laifi makirci ne kawai aka shirya hakan ya sanya ta fara rarrashin Yusura a haka har Yusura ta kwantar da hankalinta har ta hadu da wani saurayin Nazir (Sadik Sani Sadik) suka fara soyyaya dakyar Yusura ta amince masa saboda dalilinta na rashin jin dadin auren baya data yi, a hankali Nazir yana lallabata har suka yi aure. a bangaren Gidan Alhaji Sa’idu kuwa Hajiya Salma sai ta fara ganin masifa asara acikin dukiyarta har ya zamto bata da komai ta tafi wajen malaminta sai ya yi istihara ya fadamata cewar akwai abinda tayi wa Allah na sabo idan bata je ta gyara ba zata cigaba da ganin masifa a lokacin Hajiya Salma ta dawo gida cikin tashin hankali ta fara tonawa kanta asiri ashe dama itace ta hayi wannan katon ya shiga dakin Yusura ya yi mata wannan sharrin saboda dalilinta na cewar wataran ta taba samun Yusura ta fadamata cewar ta bata hadin kai duk wasu muhimman takardun Alhaji da kadarorinsa da kamfanunuwansa su dawo wajenta idan ya mutu ita ma sai ta bata nata kason amma Yusura taki amincewa wannan dalilin ne yasa ta hadawa Yusura wannan makircin saboda taci dukiya ita kadai duk da ita tasaka aka aureta, a lokacin Alhaji Sa’idu ya fara nadamar abinda ya yiwa Yusura abisa rashin sani sannan ya yiwa Hajiya Salma saki uku.

A bangaren Yusura kuma ta fara rashin lafiya suna zuwa asibiti likita ya tabbatar musu da cewar Yusura tana da ciki kuma ya fadamusu watannin cikin sai suka ga ai watannin cikin yafi karfin watannin aurensu hakan tasa suka shiga rudani da suka dawo gida suka nutsu sai suka tabbatar cikin na Alhaji Sa’idu ne kwanciya ya yi shiyasa Yusura bata san dashi ba a take aka buga waya aka shaida wa Alhaji Sa’idu ya fara murnar ashe shima zai ga jininsa.

Abubuwan Birgewa:

1- Fim din ya yi kyau kuma ya yi ma’ana sannan ga darasi da sako mai karfi a labarin.
2- Labarin ya sami tsari mai kyau sannan marubucin ya yi kokari gurin saka rikici kala-kala aciki wanda zai rike mai kallo
3- An samar da kayan aiki masu kyau kamar camera da daukar hoto da abin daukar sauti da kuma gidaje wanda suka dace da labarin.

Kurakurai

1- Akwai gurin da likita ya mikawa Hajiya Salma takarda ta sakamako bayan ya gama yi mata gwaje-gwaje sai aka ga ta bude ta karanta kuma ta fuskanci abinda yake ciki hakan bai kamata ba shine ya kamata ya yi mata bayani domin aikinsa ne kuma musamman irin wannan gwaje-gwajen fahimtarsa sai ahalin abin ma’ana wanda suka karancin fannin domin karatun likita ba abune wanda za’ayi masa taka haye ba.
2- Akwai guraren da akaga Alhaji Sa’idu ana bugomasa waya amma akan screen din wayar sai aga sam bai nuna waya ake amsawa ba kamar gurin da aka bugo masa waya aka shaida masa cewar Hajiya Salma bata da lafiya da kuma gurin da aka ga likita ya kirawoshi akan cewar cikin jikin Yusura na sane don a wannan hoton ma yafi nunawa kuru-kuru.
3- A matsayin Yusura yanda aka nuna macece mai gaskiya mai kuma fadar gaskiya amma sai aka ga wani waje kawarta ta kirawota a waya da alamun kawar jiranta take sai akaji Yusuran tace ai har ma tafita saboda haka ga tanan zuwa alhalin mai kallo a gida yaga Yusura ba a waje ba.

4- Radar da aka ga Hajiya Salma ta yiwa Nura Ajasu ‘yar maganar da sukayi ta sakwanni bai ci ace tayi masa wannan dogon bayanin ba lokacin ya yi kadan domin maikallo ya fuskanci babu abinda suka ce.

5- Shin dama can Hajiya Salma ta san Nura Ajasu ne yana yi mata wasu ayyukan? a yanda aka nuna kamar sun jima da sanin juna har aka ji yana cewa Hajiyarmu amma kuma a farkon fim din an nuna Hajiya Salma mutuniyar kirki ce tunda har tasa aka auri Yusura daga baya idonta ya bude ta canja hali shin yaushe ne ta hadu da Nura Ajasu kuma ta wana dalili?
6- An ga mahaifiyar Yusura tana ta kai kawo akan Yusuran taki yin aure duk da Yusura marainiya ce shin bata da kowa a dangin mahaifi? domin a wannan bagiren jajircewa bata mahaifiyar Yusura ce kadai ba yakamata ace an ga Namiji a jajircewar ko da kanin mahaifin Yusura ne ko kuma aji an fadeshi.

Karkarewa:

Fim ya yi kyau kuma ya yi ma’ana amma a karshe yakamata aga makomar auren Yusura duk da an san babu aure saboda ciki amma ba kowa ne zai fahimci hakan ba yakamata a budewa maikallo karshen. Wallahu a’alamu!

Share this


Author: verified_user

0 Comments: