Monday, 14 May 2018
Sharhin Fim Din "Ranar Aurena"

Home Sharhin Fim Din "Ranar Aurena"
Ku Tura A Social Media
09097438402  habibsaddika@gmail.com

Suna: Ranar Aurena

Tsara labari: Yakubu M Kumo

Furodusa: Abdul Amart

Bada Umarni: Ali Gumzak

Kamfani: Abnur Entertainment

Jarumai: Ali Nuhu, Adam M Adam, Isa I Isa, Mustapha Musty, Asiya Ahmad, Garzali Miko, Asma’u Sani, Salisu Chali, da Babangida Jalingo.

Sharhi: Saddika Habib AbbaA farkon fim din an nuna taron bikin Nasir (Ali Nuhu) da Jamila (Asiya Ahmad) a na rawa a na waka a na gwangwajewa, ango ya na yin waka da kansa, abokansa su na ta ya shi rawa. Bayan nan an nuna Nasir a gidansa ya tare tare da amaryarsa a daren ranar angoncin, an nuna ya hawo wa kan bene gurin da dakin amaryarsa ya ke ya shiga ya umarce ta da su sauko kasa, domin ta raka shi sallamar abokansa, sannan ta taya shi yi mu su godiya, saboda hidimar biki da su ka sha. Jamila ba ta yi ko musu ba ta tashi ta bi angon nata su ka fito.

Sun zo matattakalar bene su na saukowa sai Nasir ya yi tuntube ya fadi. Jamila ta kwalla kururuwa; abokan su ka ji su ka taho a guje. Su na zuwa su ka tarar Nasir tuntuni ma ya riga ya sume. Su ka dauke shi ranga-ranga su ka ta fi asibiti. Su na zuwa likita ya yi gwaje-gwajensa ya tabbatar mu su da cewar kashin bayansa ya sami matsala. Sakamakon haka daga kugunsa zuwa kasa ya daina aiki.

Jamila tare da abokan Nasir suka shiga cikin tashin hankali su ka dauko shi su ka dawo da shi gida. Jamila ta fara jinyar sa tare da kaninta, Habib. Duk abinda ya ke so shi su ke yi ma sa. Ba su taba gazawa ba har tsahon shekara guda, kuma a tsahon shekara gudar nan Jamila ta na fita aiki, domin a yadda a ka nuna tun kafin su yi aure da Nasir ta ke yin aikin.

To, wannan aikin da ta ke fita sai Nasir ya fara zargin ta a kan ko ta na kula wani a waje sakamakon shi ba wani amfani ya ke yi ma ta ba tunda ba shi da lafiya. Nasir ya fara canja ma ta ya na ta yi ma ta kananan abubuwa, ta na shanyewa har sai da wataran maigidan Jamila a gurin aiki, wato darata din kamfaninsu, ya gan ta a hanya za ta tafi gida, ya rage ma ta hanya ya kai ta gida. Daga nan ya shiga cikin gidanta, domin ya duba mijinta. Su na shiga sai Nasir ya kara tabbatar da zargin sa a kan cewa, ta na kula wani. Ya kare mu su ta tas! har ya sake ta.

Tun lokacin da Nasir ya saki Jamila rayuwarsa ta fada cikin garari. Ba shi da mai kulawa da shi, mahaifiyarsa ta kawo ma sa kannensa, mace da namiji, domin su dinga kulawa da shi, amma dukkaninsu su ka gaza; ba sa yi ma sa abinda ya ke so a kuma lokacin da ya ke so, sabanin yadda Jamila da kaninta, Habib, su ke kulawa da shi a baya.

Har sai da ta kai mahaifiyarsa ta gaji ta zo ta dauke shi ta mai da shi gidanta ta na cigaba da kulawa da shi. A lokacin Nasir ya fara nadamar rabuwa da Jamila. Ita kuwa Jamila duk da sun rabu, amma ta na cigaba da bibiyar lamarinsa. Ta je gurin likitansa ta tambaye shi ko zai iya yiwuwa a yi ma sa aiki lafiyarsa ta dawo? Likitan ya ce ma ta, a na yi, amma sai a kasar waje.

Jamila ta tafi ta je ta sayar da gidanta na gado da wasu kadarorinta ta hada ta ba wa abokan Nasir Naira milyan 30 su ka fita da Nasir kasar waje a ka yi ma sa aiki ya sami lafiyarsa ba tare ya san wane ne ya biya ba.

Sai bayan sun dawo su ke fada ma sa. A nan ya kara nadamar abinda ya yi ma ta, sannan ya tafi gidansu a kan amai da aurensu. Sai mahaifiyarta fafur ta ki amincewa. Ya tura abokansa, ta ki amincewa, Ya tura mahaifiyarsa, ta ki amincewa, domin mahaifiyar Jamila ta ce ‘yarta ba za ta koma ba tunda ya yi mata mummunan zargi na zina. A haka har mahaifiyar Jamila ta aurar da ita ga wani a cikin zawarawanta. Nasir ya kara shiga cikin matsananciyar damuwa.

A ranar da Jamila ta tare da mijinta saboda halin da ta ke ciki na tunanin Nasir ya zama na babu abinda ta ke yi sai kuka. Mijinta ya na ganin haka ya tabbatar cewa zuciyar Jamila ba ta tare da shi. Hakan ta sa a daren ya sauwake ma ta. Bayan ta dawo gida, da safe mahaifiyarta ta ci ma ta mutunci ta kuma tabbatar ma ta cewar ba za ta koma gidan Nasir ba.

Sai daga baya Habib ya je ya sami Nasir ya ba shi shawara a kan akwai wani

Share this


Author: verified_user

0 Comments: