Monday, 7 May 2018
Shahararren Jarumin Kannywood Sani Moda Na Fama Da Rashin Lafiya

Home Shahararren Jarumin Kannywood Sani Moda Na Fama Da Rashin Lafiya
Ku Tura A Social Media
Saratu Gidado da Hamisu Iyantama da shugaban hukumar tantance fina-finai ta jihar kano sun kai masa ziyara a asibitin da yake jinya a garin kaduna

Shahararren tsohon jarumin dandalin fina-finan hausa Sani Idris wanda aka fi sani da Moda ya jinyar rashin lafiya a wata asibiti dake jihar kaduna.
Jarumin shirin 'Wasila' ya shaharen a fagen masana'antar Kannywood musamman a yanayin ire-iren matsayin da yake fitowa. Ya shahara ne a fitowa a matsayin mai ruruta gaba a fina-finai.


Kamar yadda jaruma Saratu Daso ta sanar a shafin ta na Instagram yayin da ta kai masa ziyara a asibitin da yake kwance, jarumar ta sanar cewa yana fama da ciwon suga wanda aka kira da Diebetes a turanci.

Banda saratu Daso, shugaban hukumar tantance fina-finai na jihar kano,  Alhaji Isma'il Afakalla  tare da tsohon jarumi Hamisu Iyantama, sun kai ziyarar duniya ga tsohon jarumin a asibitin da yake jinya.

Tun ba yau ba Moda ke fama da wanan rashin lafiya, muna masa fatan samun sauki cikin gaggawa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: