Tuesday, 1 May 2018
Martanin OZIL Yayin Da Aka Jefe Shi Da Biredi

Home Martanin OZIL Yayin Da Aka Jefe Shi Da Biredi
Ku Tura A Social Media


Martanin da dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafar Arsenal, Mesut Özil’s ya mayar ga magoya bayan kwallon kafa, yayin da suka jefe shi da biredi ya jawo masa yabo. Bayan ya sumbaci biredin tare da dora shi bisa kansa, sai ya aje biredin a kasa cikin hankali da nutsuwa.

Abun ya auku ranar Alhamis a filin wasan emirate, yayin gudanar da wasan kusa da karshe wanda kungiyar Arsenal ta buga 1-1 da kungiyar Atletico Madrid a gasar cin kofin Europa.

Lokaci kadan bayan jifa da biredin, a minti na tamanin da biyu, sai aka ji sowa mai karfi ta jinjina daga bangaren magoya bayan Atletico Madrid, duk da kuwa da yawa daga cikin su basu san dalilin da ya sa ya aikata hakan ba.

A matsayinshi na Musulmin kasar Turkiyya, Ozil yana ganin wulakanta abinci a matsayin wani abu da addininin Musulunci ya hana, saboda an amince da cewar abinci rahama ne daga Allah.

Abin da ya aikata ba ko kokonto ya nuna godiya da yabawa da abincin da suka bashi.

An bada rahoton Ozil yana yin sallah 'yan sakanni kafin fara kowanne wasa da zai buga, sannan ba da jimawa ba ya fitar da hotonsa a kasa mai tsarki, Saudi Arabia.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: