Sunday, 6 May 2018
Kasar Saudiyya Zata Gina Coci- Coci A Dukkan Fadin Kasar

Home Kasar Saudiyya Zata Gina Coci- Coci A Dukkan Fadin Kasar
Ku Tura A Social Media


Masarautar kasar Saudiyya sun shiga wata yarjejeniya da mazhabar addinin kirista ta Vatican domin gina masu coci-coci a dukkan fadin kasar kamar dai yadda gidan yada labaran Beritbart ya rawaito

Sheikh Mohammed bin Abdel Karim Al-Issa ne dake matsayin babban Sakataren hadakar kungiyar muslmin duniya ta Muslim World League a turance da kuma Cardinal Jean-Louis Tauran, dake matsayin shugaban kungiyar mazhabar kiristocin Vatican sune suka sanya akan yarjejeniyar.

Wannan dai na guda daga cikin matakan da yarima Bin salman ke dauka domin maida kasar saudiya daidai da zamani.

Sources:Nijeriyamu a Yau

Share this


Author: verified_user

0 Comments: