Ina Nan Da Raina Ban Mutu Ba, Cewar Sani Moda


Daga Aliyu Ahmad

A yayin zantawar da RARIYA ta yi da shahararren jarumin finafinan Hausan nan Idris Sani Moda ta waya,ya karyarta jita-jitar dake ta yaduwa cewa ya rasu a daren jiya Litinin.

Sani Moda ya kara da cewa ya yi mamakin yadda labarin mutuwar tasa ta yadu, wanda a dalilin hakan yake ta faman shan kira daga ciki da wajen kasar nan. Sannan ya kara da cewa yana kan samun sauki.

Rahotanni sun nuna cewa asibitin da Moda yake jinyar ne suka yi kuskuren fitar da sanarwar mutuwarsa. Bayan wani na kusa da gadon da Modan ke kwance ya rasu.

Share this


0 comments:

Post a Comment