Friday, 18 May 2018
Gwarzon Kannywood "Ban Taba Tunanin Zan Zama Gwarzon Shekara Ba", Isa A Isa Yayi Farin Cikin Samun Lambar Yabo Wanda Yayi Takara da fitatun Jarumai

Home Gwarzon Kannywood "Ban Taba Tunanin Zan Zama Gwarzon Shekara Ba", Isa A Isa Yayi Farin Cikin Samun Lambar Yabo Wanda Yayi Takara da fitatun Jarumai
Ku Tura A Social Media

Isa A. Isa wanda ya kwashi tsawon sama da shekaru 20 ana damawa dashi a masana'antar fim, yayi murna na samun wannan kyuatar wanda ya zamanto mafi girma a gareshi a duk tsawon zaman sa a masana'antar.

Jarumi kuma mai shirya fim a masan'antar Kannywood, Isa A. Isa wanda yayi nasarar zama gwarzon shekara a bikin karrama mawaka da yan wasan arewa, ya nuna farin cikin sa bisa girmamawar da aka bashi.

Gasar Arewa Music and movies award (Amma), gasa ce wanda ake shiryawa a ko wani shekarar domin karrama fitattun jaruman da mawakan Arewa da suka taka rawar gani a sana'ar su.

Isa A. Isa wanda ya kwashi tsawon sama da shekaru 20 ana damawa dashi a masana'antar fim, yayi murna na samun wannan kyuatar wanda ya zamanto mafi girma a gareshi a duk tsawon zaman sa a masana'antar.

Yayi mamakin yin nasarar lashe kyautar a gasar wanda aka hada shi takara da Lawan Ahmed da Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa da Ado Ahmed Gidan Dabino.

Hirar shi da BBC, Isa A. Isa ya bayyana yadda ya samu nasarar bisa rawar da ya taka a shirin fim mai take "Uwata ce".

"Toh a gaskiya na tsinci kaina cikin wani farin ciki da ban ta ba zata zan samu a rayuwa ta ba saboda lokacin da na je wurin ance na fito a cikin jerin mutane bakwai da suka tsaya takarar kuma ban taba kawo wa ni zan samu ba" inji shi.
Kokarin da ya taka a cikin shirin yasa aka mika masa lambar yabon. A bisa bayanin sa, anyi nazarin kan ko zai iya daukar matsayin na shirin "Uwata Ce" domin anyi tunanin bada matsayin ga wasu fitattun jarumai kamar Sadiq Sani Sadiq ko Ali Nuhu.

"Lokacin da aka kawo labarin, ni sai na ga wurin ya dace dani. Wasu suna cewa ba zan iya ba, in karbi matsayin Sadiq Sani Sadiq. Ni fita a matsayin a sa Ali Nuhu a wancan matsayin. Sai nace kubari kugani idan Allah ya yarda zan bada abun da ake so" , yace.

Kamar yadda ya bayyana, shirin "Uwata ce" shiri ne wanda ke isar da sako kan manyan mata masu "Budurwar zuciya" kana shiri ne mai ban tausayi.

Yace za'a saki shirin ga jama'a a lokacin bikin karamar sallah.

Anyi bikin gasar AMMA a wajen taro na Soli center dake na garin Katsina a ranar hutun makon da ya shude.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: