Sunday, 6 May 2018
Fitaccen mawakin Kannywood Nazir Ahmad ya tabbatar da soyayyar sa ga shahararrar Jaruma, Gabon

Home Fitaccen mawakin Kannywood Nazir Ahmad ya tabbatar da soyayyar sa ga shahararrar Jaruma, Gabon
Ku Tura A Social Media

Shahararren mawakin nan Naziru Ahmad, ya bayyana matsayin alakarsa da fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a cikin wata hira ta musamman da yayi da jaridar Aminiya.

Da aka tambaye shi menene alakarsa da Hadiza Gabon, sai ya kada baki yace tabbas suna soyayya da juna, kuma suna matukar son juna ba wai bane, 
Naziru bai tsaya nan ba, ya cigaba da cewa:
“Mutum ba zai ce ya yi asara idan yana soyayya da ita ba. 
Amma a zahirin gaskiya ba a sa ranar auren mu ba, komai na Allah ne”-Inji shi.

Sai dai a yayin tattaunawar, mawakin ya musanta batun da ake yadawa na cewa wai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bashi kyauytar kudi naira miliyan 50 biyo bayan wata waka da yayi masa, inda yace ba gaskiya bane,“Amma ba zan bayyana abinda ya bani ba.”Inji shi.

Dayake karin haske game da yadda ya tsunduma waka, Naziru ya bayyana cewa ya fara waka ne a shekarar 2002, inda yace zuwa yanzu yana hasashen adadin wakokin da ya rera a tun bayan fara waka gadan gadan sun kai 300.

Daga karshe ya bayyana cewar duk a cikin wakokinsa ya fi kaunar wakar ‘Dan Adalan Mubi’ da kuma ‘Sardaunan Dutse’, musamman saboda a cewar sa duk abinda ya fada a cikin wakokin ya gansu a zahiri, wasu kuma ya ji su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: