Thursday, 17 May 2018
Fatima Ganduje da mijinta Idris sunyi dirar mikiya ga wata ma'abociyar kafar sada zumunta

Home Fatima Ganduje da mijinta Idris sunyi dirar mikiya ga wata ma'abociyar kafar sada zumunta
Ku Tura A Social Media
Sukar dai bata gama gushewa ba gabanin auren nata, sai dai a wannan karon ita da mijinta sun hada gwiwa wajen mayar da martani.

Fatima Ganduje da  mijinta Idris Abiola Ajimobi basu bari ya huce ba yayin da wata ma'abociyar kafar sada zumunta ta instgram ta nemi ci ma uwargida fuska.
Tuni dai lamarin auren Fatima ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bisa yanayin shigar da tayi a abukuwan da aka shirya na raya auren. Bugu da kari, jama'a sunyi Allah-wadai da halin sakin kai da ta nuna yayin shagalin biki wanda ake zargin cewa ya sabawa al'adar hausawa.

Sukar dai bata gama gushewa ba gabanin auren nata, sai dai a wannan karon ita da mijinta sun hada gwiwa wajen mayar da martani.

Ka,ar yadda wata mai suna "Auntykwalba" ta wallafa ani hoton Fatima a Instagram tare da  rubuta a shafin ta "Gaskiya anyi asaran kudin sadakan izufi
Bari inga wani shegen yazo ya CE mun rayuwarta ne a kyaleta shashashan banza munafukan addini kuma inji wani yace a cikin gida ne bcos i have posted earlier tana cikin mota da Kayan.
                                Lamarin dai bai yi masu dadi ba inda ita Fatima ta mayar da martani da "bai yiwuwa kana gulma kana kuma azumi a lokaci daya saia dai ka zabi daya a ciki".

Ba'a tsaya nan ba, mijinta Idris ya fara mayar da martanin cikin harshin yarbanci inda ya rubuta "Bride price Iya baba e lo waste".

Bayan ga nasiha da jan hankali da Auntykwalba tayi kan shigar da matar a tayi wanda ya sabawa al'adda da addini, Idris ya bayyanar mata da abun dake cikin zuciyar shi.
Ya mayar mata da martani inda ya rubuta "Ni ina girmama wanda yake girmama kansa kuma ita girma a siyan ta balle a haifi mutum dashi. Aikin mutum ke samar masa shi.

Idan ba'a manta ba, bikin auren ya janyo tsaigumi da suka daga malaman addinin da wasu daga cikin yan wasan masana'antar kannywood.

Jama'a sun nuna bacin ran su game da yadda angon da amaryar suke runguma a bainar jama'a.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: