Tuesday, 29 May 2018
Dalilin Da Yasa Bani Shiga Fina Finan Kudu ba wato (Nollywood) -Inji Fati Shu'uma

Home Dalilin Da Yasa Bani Shiga Fina Finan Kudu ba wato (Nollywood) -Inji Fati Shu'uma
Ku Tura A Social Media
Fati Shu’uma, jarumar wasan fina-finan Hausa mai haskawa, ta bayyana cewar tsananin kishin da take yiwa kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood ne ya saka ba zata shiga shirin fina-finan yaren Turanci da ake shiryawa a kudancin Najeriya ba.

Jarumar ta fadi hakan ne ga wakilin gidan Radiyon BBC, Mansur Abubakar, yayin daukar wani sabon shiri mai suna Makanta Biyu.

Ali Nuhu da Rahama Sadau na daga cikin jarumar fina-finan Hausa dake fitowa a shirin fim din Turanci na kudancin Najeriya.


Fati Shu’uma da Ali Nuhu yayin daukan shirin Makanta Biyu
A cikin fim din Makanta Biyu, Fati Shu’uma, ta fito a matsayin makauniya wacce ta sace zuciyar wani attajiri, Ali Nuhu, wanda son ta ya kama shi.

Ali Nuhu ya koma daukan dawainiyar tad a ta iyayen ta saboda son da yake mata, kafin daga bisani ya biya kudin yi mata maganin makantar dake damun ta.Saidai Bayan Fati ta warke sai ta juyawa Ali Nuhu baya tare da sabawa umarnin iyayen ta na auren shi.

Daga baya an aurawa Ali Nuhu kanwar Fati, ita kuma makantar ta dawo.

Wanda ya shirya fim din, Hamza Abubakar, y ace sakon dake cikin shirin it ace nuna illar rashin biyayya ga iyaye. Ana saka ran shirin zai fito kasuwa nan da watanni biyu zuwa uku.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: