Saturday, 26 May 2018
Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah

Home Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah
Ku Tura A Social Media
Shahararen dan kwallon nan Muhammad Salah ya bayyana cewa duk da cewa yanzu lokacin azumi ne kuma ga wasan karshe na cin kofin zakarun turai bazai iya ajiye azumi ba saboda kwallon kafa.

Salah ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a shirye shiryen da kungiyarsa ta Liverpool tkeyi na buga wasan karshe da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a ranar Asabar.

A baya ana ta zuba ido ko dan wasan ya ajiye azumi a ranar Asabar saboda wasan na karshe domin ya samu kwarin gwuiwa da kuma karsashi a wasan da zasu fafata.Sai dai rahotanni daga kasar Masar sunce dan wasan zaici gaba da yin azuminsa har zuwa ranar wasan kuma zai fita yayi wasansa batare da rashin karfi ba kamar yadda ake zato.


Wannan ba shine karo na farko da jarumin ke nuna jajirewa akan addininsa ba.
 zuwansa wani tsohon masallaci a Liverpool ya kara yawan mutanen dake halartar masallacin wanda ya hada da matasa da kuma tsofaffi, wanda ya kara daga martabar addinin musulunci a fadin kasar.

Dr. Abdul Hamid daya daga cikin malaman masallacin na Sheikh Abdullahi Quilliam yace matasa na ta kara tararowa masallacin suna gabatar da salloli a ciki harda sallar juma’a saboda Mohamed Salah, na zuwa masallacin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: