Monday, 7 May 2018
Ado Gwanja Babu abun da ya shiga tsakani na da Adam A.Zango kana na daina fitowa a matsayin dan daudu

Home Ado Gwanja Babu abun da ya shiga tsakani na da Adam A.Zango kana na daina fitowa a matsayin dan daudu
Ku Tura A Social Media
Fitaccen jarumin wasan barkwanci kuma shahararen mawaki Ado Gwanjo, yayi karin haske game da alaka dake tsakanin sa da jarumi Adam A.Zango.
Jita-jitra dake yaduwa a kafafen sada zumunta na cewa jarumai suna takun saka tsakanin su.

Hirar shi da jaridar Premium Times, Ado Gwanja yayi karyata jita-jitan tare da bayana hakikanin alaka dake tsakanin sa da tauraron Kannywood.

Yana mai cewa " Kasan ba a rasa wadanda basu rasa abin cewa a kullum. Su bi wurare suna fetsa maganganu iri-iri. Amma ni dai a sani na babu abin da ya shiga tsakani na da Adam Zango. Hasali ma shi maigida na ne domin ni a yaron sa na fara sana’a ta kuma har yan zu ma haka ne.

Jarumi  wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin dan daudu a fim, ya bayana cewa zai daina fitowa a matsayin haka. Yace daga yanzu matsayin barkwanci kawai zai dinga fitowa a cikin fina-finai.

" A’a yanzu kam na dai na fitowa a fina-finan da zai haska ni a matsayin dan daudu. Zan tsaya a barkwanci na kawai" yace.

Yayi ma dinbim masoyan sa godiya bisa soyayar da suka nuna masa game da wakokin sa kana yana masu albishiri cewa zai cigaba da nishadantar dasu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: