Sunday, 20 May 2018
Adam A. Zango ya nuna soyayyar sa a fili ga Zainab Indomie Karanta

Home Adam A. Zango ya nuna soyayyar sa a fili ga Zainab Indomie Karanta
Ku Tura A Social Media
Daya daga cikin taurari kuma fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sannan kuma shahararren mawakin Hausa din watau Adam A. Zango ya fito fili ya nunwa duniya irin yadda yake da matukar kyakkyawar alaka da jarumar nan Zainab Indomie.

Tauraron na fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango din dai ya saka wani hoto ne nasa kenan tare da tauraruwar fim din ta Hausa da tauraruwar ta ta dan lafa, Zainab Indomie a shafin sa na sada zumunta na Facebook.

Adamu din ya bayyana cewa yana tare da ita cikin daukaka da rashinta, cikin arziki da talauci, ya kare da cewa "Allah yi miki Albarka Indo."

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya tauraruwar Zainab ta haska sosai a duniyar fina-finan Hausa amma sai aka dena jin duriyarta, inda wasu ma har suka rika yin surutai iri-iri akan musabbabin abinda ya sa aka daina jin duriyar Zainab ciki hadda wanda aka rika cewa ciwon kanjamaune ya kamata.

Amma dai jarumar daga baya ta fito ta karyata hakan harma tayi Allah ya isa ga duk wanda suka mata wancan kazafin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: