Kannywood

Abubuwa Da Ya kamata A Sani Game Da Marigayya Hauwa Maina

Masana’antar Kannywood tayi babbar rashi, rasuwar fitacciyar jaruma Hauwa Maina.
Jarumar ta rasu daren ranar laraba 2 ga watan Mayu » , a asibitin Malam Aminu kano inda take jinya bayan wata rashin lafiya da tayi.

Ga takaitaccen tarihin rayuwar ta:

Haifafiyar yar garin Biu na jihar borno, an haife Hauwa Maina a cikin shekarar 1970.
Tana fara haskawa a cikin shirin fim a shekarar 1999. Fim na farko da ta fara fitowa a ciki shine tuba wanda tsohon ma’aikacin NTA, Musa Yahaya ya bada umarni.
Kamar yadda ta shaida, a farko dai iyayen ta sun nuna rashin jituwa da sana’ar da ta zaba sai dai daga baya sun amince ta cigaba da harkar fim ganin irin fa’idar da yin haka yake da ita ga cigaban al’umma.

Banda fitowa a fim, Hauwa Maina tana bada umarni tare da shirya fim, tayi karatu kan wannan ilimin a kasar Amurka.
Ta dauki nauyin shirya wasu fina-finai karkashen kamfanin ta mai suna Ma’inta Enterprise Limited.

Hauwa maina tare da diyar ta maryam

A tsawon shekara 20 da tayi a masana’antar fim, marigayya ta haska a fina-finai fiye da 50 masu kayatarwa. mafi birgewa cikin fina – finai da ta taka rawar gani akwai fina-finan tarihi kamar, ‘bayajidda’ da ‘Queen Amina’.
Banda fina-finan hausa ta Kannywood, jarumar ta haska a cikin fina-finan nollywood da dama.

A wata hira da tayi, ta sanar cewa bata karban aikin fitowa a fim matukar bata gamsu da labarin shirin musamman idan bata da ma’ana ko bata ilmantarwa.
Allah ya albarkace ta yara biyu Maryam da Abdulrahman.
Diyar ta Maryam wanda ta shahara a fagen wake kuma daya daga cikin matasa dake jajircewa wajen daukaka addinin musulunci.

Hauwa maina tare da Ali nuhu

Kamar yadda hauwa maina ta shaida, akwai kyakyawar dangantaka tsakanin ta da diyar ta domin mafi yawancin lokaci bata yin wata aiki ba tare da ta nemi shawarar ta ba.
Hakika wannan dangantakar tasu yayi kaurin suna kana hakan ya bayana ga bainar jama’a yayin daurin auren diyar. Jarumar tayi sharara hawayen ga bikin ganin cewa zata rabu da aminiyar ta.

Ta kasance tamkar uwa ga sauran jaruman Kannywood.
Mafi yawancin abokan sana’ar ta ta kannywood na girmama ta. Ta kasance tamkar uwa ga sauran jarumai.
Rasuwar ta ya girgiza mutane da dama na Kannywood tare da dinbim masoya da masu bibiyan fina-finan hausa.

Jarumai da dama sun yi jimamin rasuwar ta inda suka wallafa hotunan ta a shafukar su na kafafen sada zumunta tare da yi mata fatan Allah ya jikan ta da rahama.
Hakika Kannywood tayi babbar rashi kuma samun wacce zata maye gurbin ta zaiyi wuya.
Muna fatan Allah ya jikan ta da rahama, ya kuma gafarta mata.

Sources :pulse.ng

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button