Kannywood

Abinda Ke Tsakanina Da Jarumi Adam A Zango – Amina Amal

Bayan fim din ‘Amal’ kin yi fina-finai kamar nawa?

Bayan ‘Amal’ na yi fina-finai sun kai bakwai zuwa takwas. Bayan ‘Amal’ na fito a ‘Hisabi’ da ‘Matan Aure’ da ‘Abu Hassan’ da ‘Basaja Gidan Yari’ da ‘Ramlat’ da sauransu.

A cikin wadannan fina-finai, wanne kika fi so?

Na fi son ‘Amal’, domi shi ne fim dina na farko, kuma shi ya daga ni a duniyar fina-finan Hausa.

Wani fim kika fi shan wahala lokacin daukarsa?

Na fi shan wahala a fim din ‘Amal’, dalili kuwa shi ne ba a taba dora mini kyamara sai a fim din ‘Amal’, kuma jarumin da aka hada ni da shi babban jarumi ne wato Zango, kuma yana yi mini kwarjini, idan daukar ba ta shafi fitowa da shi ba, to zan bayar da abin da ake so, amma daukar da nake tare da shi sai in kasa magana, in rikice, to a fitowa daya sai mu yi kamar awa biyu, haka za a yi ta yi wani lokaci kowa yay i fushi, amma haka yay i ta hakuri da ni har aka kammala daukar fim din.

Yaya soyayyar da kike yi wa Adam A. Zango ta kasance bayan kin zo Najeriya, idan aka kwatanta da wacce kike yi masa a lokacin da kike Kamaru?

Soyayyata tana nan sai karuwa take yi, soyayyar ya da kanwa muke yi wa juna, ba soyayya ta soyayya ba, ya dauke ni a matsayin kanwarsa, ni kuma na dauke shi a matsayin yayana. Ka ga kuma babu soyayya tsakanin ya da kanwa.
Ganin yadda kika yi abubuwa a kansa, har kika bar kasarki Kamaru kika zo Najeriya don shi, ko za ki iya sadaukar da rayuwarki don shi?
Zan iya sadaukar da rayuwa don shi, domin ya yi mini gata, ya karbe ni hannu biyu, ya kyautata mini, ya kuma dauke ni kamar ’yar uwarsa ta jini.

Wane ne ubangidan Amina Amal a Kannywood?

Iyayen gidana biyu ne a Kannywood, na farko Abu Sarki, sai na biyu Adam A. Zango.
Me za ki ce kan batun jita-jitar da ake yadawa cewa akwai soyayya mai zafi tsakaninki da Abu Sarki, wanda shi ne furodusan fim dinki na farko wato ‘Amal’?
A gaskiya babu soyayya, jininmu ne ya hadu, kuma mun shaku da juna sosai, don haka mutane da yawa suna ganin muna soyayya, amma shi ma dai yayana ne.
Zuwa yanzu za a iya cewa ko burinki ya cika a harkar fim?
Burina bai gama cika ba, saboda ban kai inda nake so in kai ba, na biyu kuma ina so in zama kamar jaruma Hadiza Gabon, ko Fati Muhammad, ka ga kuma ban kai wannan matakin ba, ko ma rabi ma ban kai ba.

Wani bambancin rayuwa kika samu bayan kin fara yin fim?

A wurin da na taso ni mutum ce mai son ’yanci da kuma watayawa ko sakewa, zan je kasuwa, amma yanzu bayan na fara fim ba ko’ina zan je ba, akwai ranar da na je kasuwar bacci a Kaduna aka kusa kashe ni, don kowa yana so ya gaishe ni, ko kuma mu dauki hoto, turmutsutsin mutane ya sanya numfashina ya dauke, wani ya ja hannuna sai da na kusa mako guda yana mini ciwo, su a wurinsu soyayya ce, ni kuma abin ya cutar da ni, a yanzu babu sakewa idan aka kwatanta da lokacin da ban fara fim ba.
Ko za ka iya tuna wani abu na tsoro ko firgici da ya faru da ke dalilin harkar fim?
Ban samu kaina a wani abu makamancin haka ba.


Kwanan nan kin je Legas, shin ko harkar fim ce ta kai ki can din?

Abubuwa da yawa ne suka kai ni Legas, amma idan lokaci ya yi to mutane za su san abin da ya kai ni Legas din, amma yanzu ban kammala abubuwan da suka kai ni Legas ba.

A kwanakin baya an ga hotonki da wasu matsattsun kaya a shafinki na Instagram, inda hakan ya haifar da cece-kuce, ko yaya aka yi kika sanya hoton a shafin naki?

Ka san lokacin da hoton ya fito ban ce komai ba, amma da yawa mutane sun kira ni, kowa kuma fada yake yi mini, amma ban samu na yi wa kowa bayani ba, dalili kuwa shi ne, ba kowa ne zai fahimce ni ba, kuma hoton ya fito a shafina ne, ko na yi bayani za a ga kamar kirkira na yi, shi ya sa na yi shiru, wannan hotona ne, wata kawata ce ta dauki wayata da ma tana da lambobin sirrin wayata, ina da kusanci da ita sosai, ba na so in ambaci sunanta, sai ta dora hoton a Instagram, ni ban ma san ta dora ba, sai na ji ana ta kira na, inda jama’a suka rika tambayata dalilin da ya sa na dora wannan hoton, daga nan ne na cire hoton, amma kafin nan dubban mutane sun gani, wasu har sun saukar da hoton a wayoyinsu, kuma ba ni da hujjar da zan ce ba ni na dora hoton ba, saboda a shafina aka gan shi. Ina rokon jama’a su gafarce ni, akasi aka samu

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button