Kannywood

Abin Da Ya kai Ni kasar Ghana – Jaruma Nuhu Abdullahi

Nuhu Abdullahi yana daya daga cikin jaruman fina-finan Hausa da tauraruwarsu ke haskakawa a Kannywood, a kwanakin bayan ya halarci kasar Ghana don yin aikin fim din Turanci mai suna ‘Yellow Paper’, a tattaunawar da Aminiya ta yi da jarumin ya bayyana yadda ya samu gayyatar zuwa kasar Ghana da rawar da ya taka a fim din da ya yi a Ghana. Jarumin wanda ya fito a manyan fina-finai da suka hada da ‘Gaba da Gabanta’ da ‘Ashabul Kahfi’ da kuma ‘kanin Miji’ ya bayyana dangantakar da ke tsakaninsa da jaruma Hajara Isa. Ga yadda hirar ta kasance:


A kwanakin baya ka sanya hotunanka a shafin sada zumunta na Instagram, inda ka sanya ka je kasar Ghana don daukar wani fim, masu karatu za su so su san yadda ka samu gayyata zuwa kasar Ghana?

Wani kamfani ne mai suna Pan Africa ya gayyace ni aikin fim mai suna ‘Yellow Paper’, abin da ya faru kuwa shi ne wannan kamfani ya zabo jarumai daga duk wata masana’antar fina-finai da ke Afirka, wadannan mutane sun dauki jarumi daya zuwa biyu domin su yi wannan fim din, sun zakulo jarumai daga Ghana da Afirka ta Kudu da Kwaddibuwa da Senegal da Mali da Kamaru da Najeriya da sauran kasashen Afrika.

To, kamar yadda suka kira jaruman Afirka, to ni ma su ne suka gayyace ni, sun kuma kira jaruman wadannan kasashen da a ambata sannan suka ajiye mu a lema daya, inda muka dauki fim din mai suna ‘Yellow Paper’

Yaya ka ji da wannan gayyata da aka yi maka?

A gaskiya na ji dadi, domin ban yi tunanin a dan fitowar da nake yi a fina-finai a Najeriya har ya kai cewa an gayyace ni yin fim a wata kasa ba, ban yi tsammanin za a kira ni wata kasa domin in je in taka rawa a wani fim ba. A gaskiya ina alfahari da hakan.

Shin kai kadai ne jarumin da aka gayyata daga Najeriya?

A’a, ba ni kadai ba ne daga Najeriya, amma dai ni kadai ne daga Kannywood.

Shin wace rawa ka taka a fim din?

Na fito a matsayin saurayi ne, inda nake da mahaifiya da kuma yaya, sauran abubuwan da suka faru wannan masu kallo ne za su gani da idonsu.

A kwanakin baya an fara daukar fim dinka mai suna ‘Gudun Tsira’, inda ka ware masa Naira

miliyan 10, zuwa yanzu yaya ake ciki dangane da fim din?

Ba mu kai ga kammala aikinsa ba, saboda muna so ya zama zakaran gwajin dafi a cikin masana’antar fina-finan Hausa, muna yinsa a hankali, a hankali ne, saboda muna bukatar tallafi daga kamfanoni, to akwai ragowar tallafin da ba mu kai ga samu ba, amma dai insha Allahu muna sa ran za mu samu har mu kai ga karasa fim din, kuma zai zo ga masu kallo.

Shin ka kai ga sanya lokacin da za ka kammala daukar fim din?

Ina sa ran ba zai wuce nan da wata shida ko zuwa bakwai, saboda babban shirin muke yi a kan fim din, to ba a bukatar gaggawa.

Me za ka ce dangane da jita-jitar da ake yadawa cewa akwai soyayya mai karfi tsakaninka da jaruma Hajara Isa, wadda kuka fito a fim din ‘There is a Way’?

A zahirin gaskiya babu wata soyayya a tsakaninmu, kuma duk wanda ya kalli ci gaban fim din, wato ‘This is the Way’ ke nan, an yi wadansu abubuwa sosai kuma idan har za a yi mata adalci to ita ya kamata a ce na aura a fim din, tun da ta fito a matsayin ’yar gidan attajiri, wannan dalilin ne ya sa nake tsokanarta da Mrs Isham, wato sunan da na fito da shi a fim ke nan. Amma babu wata soyayya ta zahiri a tsakaninmu sai dai mutunci.

Mene ne ra’ayinka dangane da siyasa?

A gaskiya ina da ra’ayin siyasa, amma dai ban shirya mata a yanzu ba, amma nan gaba za a fafata da ni a siyasa.

Kana daya daga cikin jaruman Kannywood da suke haskakawa, ka kuma cimma wadansu nasarori, a zuwa yanzu wadanne matsaloli kake fuskanta?

Ba zan iya cewa kai tsaye su ne matsalolin da nake fuskanta ba, amma da yake su ne matsalolin da Kannwood ke fuskanta, sai in ce nima su ne matsalolin da nake fuskanta, babbar matsalar da muke fuskanta ba ta wuce ta satar fasaha ba, kuma a matsayina na mai shirya fim, ina fuskantar matsalar satar fasaha, idan ka duba yadda ake sayar da fina-finai akwai bambanci a da da kuma yanzu, saboda masu satar fasaha suna kara yawaita fiye da tunanin mutum, kuma abin yana dawo da masana’antar baya, saboda sai ana samun kudin shiga ne za a iya inganta harkar, kuma idan kudin shiga ya ragu a hannun masu shirya fim, to abubuwa ba za su rika gudana kamar yadda aka saba ba.

Kuma dalilin satar fasaha matasa da yawa suna rasa aikin yi, ko dai aikin yana raguwa ko kuma yawan ma’aikatan na raguwa, sannan ana rage yawan kudin da aka kashewa a harkar, wannan ita ce babbar matsalar da muke fuskanta gaba daya ’yan fim.

A ganinka me ya sa aka kasa shawo kan matsalar satar fasaha?


Akwai hukuma kocokan wacce take da hakkin kare mallakar kayan mutum na fasaha ko na fim ko na littafi kai ko wani abu da ya shafi kirkira na fasaha, abin da yake faruwa shi ne hukumar ba ta yi aikinta, ba ta da wani abu face ta karbi kudin da ake biyanta a kan kayan fasaha, duk da cewa za a biya ta, amma ba ta bibiyar hakkin masu kayan fasaha.
Akwai kuma hukumar tace fina-finai ta kasa, dukkan wadannan hukumomi suna karbar kudi mai nauyi, amma ba sa bibiya domin su ga sun kare mana hakkin kayanmu. Wadannan hukumomin duk ba sa yin aikinsu yadda ya kamata, sannan kuma gwamnatin da take kai yanzu, ka duba irin gudunmuwar da muka ba ta a lokacin zaben 2015, kuma mun yi korafe-korafe ta kafafen yada labarai da kuma a rubuce-rubuce, amma dai taimakon da ake bukata domin a magance satar fasaha ya gagara. Kuma barazana ce babba saboda dimbin matasan da suke samun abinci dalilin wannan masana’anta suna ta raguwa, don haka ya kamata gwamnati ta kawo agaji, muna bukatar agajin gaggawa, matasa ne zuryan a cikin wannan masana’anta, kuma suna ta rasa aikinsu dalilin da yadda kasuwancin fina-finai ke tafiya, kasuwancin kullum kasa yake dada yi.

Idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a hakan, za a iya cewa masana’antar ta kusa durkushewa?

Gaskiya ne, ana kusa da hakan, idan ka ga irin fina-finan da ake bugawa, kusan yanzu idan ka nemi yin kididdiga, misali daga shekara daya zuwa yanzu, to babu wani kasuwancin da ake yi, kasuwancin ya tabarbare, mutane da yawa sun daina kasuwancin fina-finai, saboda masu satar fasaha sun yi yawa, kuma a zaharin gaskiya ’yan fim ba za su iya yakar su ba, saboda ba mu da jami’an tsaro, kuma ana nan ana kallonsu a gari, suna yawo, ga kuma inda suke kasuwancinsu, a gaskiya ba mu da jami’an tsaron da za mu iya hana su, ba mu da yadda za mu yi da su, sannan hukumomin da suka kamata su yi mana yaki da su ma ba sa yin abubuwan da suka kamata.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?