Friday, 20 April 2018
Yanzu-yanzu: Hukumar yan sanda ta karawa Ibrahim Magu girma

Home Yanzu-yanzu: Hukumar yan sanda ta karawa Ibrahim Magu girma
Ku Tura A Social Media
Hukumar yan sandan Najeriya a yau Juma'a ta sanar da karin girman manyan jami'an yan sanda 18.

Daka cikinsu akwai shugaban hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Hukumar ta kara masa girma daga matsayin mataimakin kwamishanan yan sanda zuwa kwamishana.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC domin yakan cin hanci da rashawa. Amma duk da hakan, majalisan dattawa ta ki tabbatar da shi saboda rikici da ke tsakaninsu.

Wannan sabon karin girma da aka masa na kunshe cikin jawabin kakakin hukumar Ikechukwu Ani.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: