Monday, 16 April 2018
Ya Kamata A Sanya Sunan Ta A Kundin Ababen Tarihi Na Duniya

Home Ya Kamata A Sanya Sunan Ta A Kundin Ababen Tarihi Na Duniya
Ku Tura A Social Media
Daga Imam A Saleh

Yayin da yawancin mata ke tsinuwa da Allah wadaran kishiya, ita kuwa wannan baiwar Allar halartar karin auren da mijin ta ke yi ta yi, har ma ta ci kwalliya ta je fuskarta cike da annuri da annushuwa kai ka ce ita ce amaryar.

Wasu suna ganin ta yi hakan ne domin a rika irin wannan yamadidin da muke yi yanzu, alabashi duniya ta yi mata kallon gwarzuwa, amma dai ni ban mata wannan kallon ba, hasalima sai na fada kogon tunanin ashe dama akwai mata masu irin wannan tawali'un?

Ina bada shawarar ya kamata a fara shirya wasu tarurrukan wayar da kan mata a rika gayyato wannan baiwar Allar ta rika yin cikakkkiyar fadakarwa kan mata su yi koyi da ita.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: