Saturday, 14 April 2018
Umee zee Ta Samu Matsayin Zama Shugaban Mata Ta Yaken Neman Zabe PDP 2019

Home Umee zee Ta Samu Matsayin Zama Shugaban Mata Ta Yaken Neman Zabe PDP 2019
Ku Tura A Social Media
Tsohuwar jaruma masana'antar kannywood Umme zee ta samu wani matsayi a babbar jam'iyar hamayya ta Nijeriya wato PDP  ga gawajin godiya daga baki jarumar

...da yardar Allah sai PDP ta karbi mulki a 2019, inji Zee Zee

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Ummi Ibrahim wadda aka fi sani da Zee Zee ta samu mukami daga jam'iyyar adawa ta PDP, inda aka ba ta mukamin shugabar riko ta mata ta kungiyar dake yi wa PDP yakin neman zabe gida-gida ta kasa baki daya.

A yayin da Ummi da take bayyana wannan labari a dandalinta na sada zumunta, tace ta godewa Allah da wannan mukami da ta samu, kuma tana fatan Allah ya baiwa jam'iyyar ta PDP mulki a zaben shekarar 2019.

Ummi dai ta yi suna wajan caccakar gwamnatin shugaba Buhari.

Wani shafi da ya wallafa wannan labari, me suna Authenticnewsdaily yace shugaban kungiyar yi wa PDPn kamfen gida-gida na kasa ne, Ibrahim Dahiru Danfulani ya tabbatar da wannan mukami na Ummi Zee Zee a jiya Juma'a.

"Godiya ta tabbata ga Ubangiji mai cikakken tsarki da yau JUMA'A ya bani babban matsayi a jam'iyyar PDP ta kasa baki daya, Alhamdulillah.

Sannan ina mika godiyata ta musamman ga 'yan PDP ta kasa baki daya, ina kuma addu'ar Allah ya bawa PDP shugabancin kasar nan a shekara mai zuwa 2019.

Nagode!
Ummi Ibrahim (Zee-Zee)

Share this


Author: verified_user

0 Comments: