Sunday, 1 April 2018
Shugaban Majalisar Dattawa zai kalubalanci Buhari a zaben 2019

Home Shugaban Majalisar Dattawa zai kalubalanci Buhari a zaben 2019
Ku Tura A Social Media
Akwai jita-jitar cewa Saraki zai yi takara da Shugaba Buhari a 2019

- Sai dai wasu na ganin aikin wasu makiya ne kurum a Jam’iyyar APC

- Har yanzu dai Shugaban Majalisar bai tabbatar da wannan magana ba

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana shirin tsayawa takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019. Sai dai wasu sun ce an fara yada labari ne kurum domin a hura wutar rikicin Jam’iyyar APC.

Jaridar Boss ta fara rahoto cewa Bukola Saraki zai nemi takara a 2019 sai kuma ga shi an ji Shugaban gidan Jaridar Ovation watau Dele Momodu yana kiran jama’a su marawa Shugaban Majalisar kasar baya a zabe mai zuwa domin yace ya cancanta.

Sai dai wata Majiya daga Jaridar This Day tace an fara yada wannan jita-jita ne domin a hada rikici a Jam’iyyar yayin da maganar kujerar Shugaban APC na kasa John Oyegun take cigaba da rawa amma babu gaskiya a maganar takarar Saraki.

Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki ya nemi takarar Shugaban kasa tun ba yau ba, kuma ko a zaben da ya wuce yayi kokarin tsayawa takarar kafin ya yanke shawarar komawa Majalusa. Har yanzu dai Saraki bai ce komai ba game da maganar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: