Sunday, 29 April 2018
Musabbabin abinda yasa Auren mata 'yan fim ke mutuwa - inji Bintu dadin kowa

Home Musabbabin abinda yasa Auren mata 'yan fim ke mutuwa - inji Bintu dadin kowa
Ku Tura A Social Media
Yayin da ta ke amsa tambayoyi game da dalilan da ke sa auren jaruman Kannywood mata ba ya dorewa, Fatima Sa’id Abdullahi wacce aka fi sani da Bintu Dadinkowa na gidan Talabijin na Arewa 24 ta bayyana cewa yawanci iyaye ne ke yin katsalandan a harkar auren.
A cewar ta, jaruman Kannywood mata na son zaman aure kuma su kan kasance mata na gari, amma saboda yadda aka bata masu suna da irin shaidar da aka yi masu, sun kan kasa samun damar zaman dindindin a gidajen mazajen su.

Ta ce yawancin lokuta za a yi aure kuma jarumar na son mijinta shi ma yana son ta, amma mutane ba za su bari su zauna lafiya ba, ta yadda za a yi ta yin ziga har sai auren ya baci.
“Yawancin lokuta iyayen mijin ne ke zama masu zugar sabda sun riga sun yanke hukunci game da sirikar ta su cewa ba ta da kamun kai saboda ita ‘yar fim ce.

Ta ce wani lokacin makota su ke ingiza iyayen ta hanyar nuna masu cewa dan su ya yi zaben tumin dare.
“Kafin ka ce miye wannan sai a ce aure ya lalace.” Inji ta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: