Wednesday, 18 April 2018
Labarin Soyayyar su Da Angota 'Ni ba Bahaushiya bace: Ina jin dadin rayuwar aurena' ~ Fatima Ganduje

Home Labarin Soyayyar su Da Angota 'Ni ba Bahaushiya bace: Ina jin dadin rayuwar aurena' ~ Fatima Ganduje
Ku Tura A Social Media

Fatima Abdullahi Umar Ganduje diyace gurin gwamnan jihar Kano wadda kwanakin baya kadan akayi aurenta da mijinta, d'a daya namiji tilo a gurin gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi,

Shekarun Fatima 24 da haihuwa, ta kammala karatunta na jami'a da digiri me daraja ta daya daga jami'ar kasar Amurka dake jihar Adamawa,

Fatima na da gidauniya data bude dan tallafawa mata da yara.

A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita,
Fatima ta amsa wasu daga cikin tambayoyin da yayi mata kamar haka:

City Poeple :- Da alama kina jin dadin rayuwar aurenki?,

Fatima :- Eh, Tabbas hakane tun bayan da mukayi aure na kasance cikin farin ciki a gidan mijina.

CP :- Shin zaki iya gaya mana yadda kuka hadu?,

Fatima :- Wannan dogon labarine amma a takaice, mun hadune sanadiyar wani dan uwanmu, kuma muna haduwa muka shaku da juna.

CP :- Zaki iya gaya mana kalmar farko da ya fara gaya miki lokacin da kuka hadu?,

Fatima :- Ya ce min zan iya sanin ko ke wace ce, sai na amsa da cewa Eh, me zai hana?

CP :- Tsawon wane lokaci kuka dauka kuna soyayya?,

Fatima :- Shekara daya da kusan rabi.

CP :- Shin zaki iya gaya mana wane irin mutum ne mijinki?,

Fatima:-  Mijina mutumin kirki ne yana kula dani kuma dukkan abinda nake nema a tattare da miji yana dashi.

CP : Shin yaya kike kina kwalliya ki fito da kyau haka, tsawon wane lokaci kike dauka kina kwalliya?,

Fatima:-  Bana wani dadewa mintuna talatin kawai sun ishe ni, saboda nasan abinda zansa ya min kyau.

CP :- Shin yaya zaki bayyana 'yan uwan mijinki?,

Fatima :- Suna son dan uwansu sosai kuma nima suna nuna min soyayya babu wani nuna banbanci.

CP :- Shin a matsayinki na bahaushiya yaya kike ji da kika auri bayerabe?,

Fatima :- Ni ba bahaushiya bace, ni bafulatanace.

CP :- Idan da ace bahaushe kika aura kina tunanin zaki samu bambancin soyayya?

Fatima :- Ai soyayya ba ruwanta da yare.

CP :- Kin iya yarabanci? ,

Fatima :-  A'a nadai dan fara koyo(tayi wani yarabanci kadan) amma ina sa ran nan gaba zan iya sosai
Kai harma abincin yarabawa duk ina so na iya.

CP:- Ya zaki bayyana uwar mijinki?,

Fatima :- Mutuniyar kirkice tana yi min abinda ya kamata, bama uwar mijin bace uwatace.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: