Thursday, 26 April 2018
Kasar Saudiyya ta bayar da gagarumar kyauta ga dan kwallon kafa Mohammed Salah

Home Kasar Saudiyya ta bayar da gagarumar kyauta ga dan kwallon kafa Mohammed Salah
Ku Tura A Social Media
Dan wasan kwallon kafar kungiyar Liverpool ta kasar Ingila, Mohammed Salah, ya samu kyautar katafaren fili daga hukumomin kasar Saudiyya saboda lashen kyautar dana wasan gasar cin kofin Firemiya na kasar Ingila da ya yi.

Fahd Al-Rowky, mataimakin shugaban birnin Makkah, ya bayyana cewar kyautar filin na matsayin taya dan wasan murna ne.

"Muna da filaye a wurare masu daraja. Duk inda ya zaba a nan ne zamu bashi filin koda kuwa daf da Harami ne kuma zamu bashi damar zabin irin ginin da yake so sannan mu gina masa," a cewar Al-Rowky.

Dan wasa Mohammed Salah ya doke abokin takarar sa Kevin De Bruyne kafin ya lashe gasar dan wasan gasar cin kofin gasar Firemiya ta kasar Ingila ta wannan kakar da muke ciki.


Dan wasa Salah na cigaba da burge masu kallon kwallon kafa a duniya musamman magoya bayan kungiyar Liverpool da kuma kasar sa ta haihuwa, Egypt.

Salah ya zurawa kungiyar Liverpool kwallo 31 a raga a gasar firemiya ta kasar Ingila tare da kara zura wasu kwallo 10 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai da ake bugawa.

Ya zuwa yanzu babu wani dan wasa dan asalin nahiyar Afrika da ya taba nuna irin wanna bajinta a duniyar kwallon kafa.

Wasu manyan tsofin 'yan kwallon kafa a duniya irin su Frank Lampard tuni suka fara kiran a saka Salah cikin masu gasar neman cin kambun zinare na ballon d'or, wato dan wasan da yafi kwarewa a taka leda a duniya.

Sources:naij.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: